Kross ya buga wa Real wasa na 450 a gidan Rayo

Toni Kross

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Toni Kross ya buga wa Real Madrid wasa na 450 a karawar da ta tashi 1-1 da Rayo Vallecano ranar Lahadi a La Liga a filin wasa Vallecas.

Ɗan kasar Jamus ya canji Camavinga a minti na 70 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da kungiyoyin suka raba maki a tsakaninsu.

Tun bayan da ɗan wasan ya koma Real Madrid da taka leda ya lashe dukkan wani kofi da ɗan wasa ke mafarkin dauka a tarihin tamaula.

Jimilla ya lashe kofi 21 a kungiyar Santiago Bernabeu da ya hada da Champions Leagues hudu da Club World Cups biyar da Uefa Super Cups hudu.

Sauran sun hada da La Liga uku da Copa del Rey da Uefa Super Cups hudu da Spanish Super Cups hudu.

Kroos tsohon ɗan kwallon tawagar Jamus, yana gaba-gaba a jerin wadanda suke buga wa Real wasa da yawa a tarihi.

Cikin karawa da ya yi wa Real 450, ya buga wasa 297 a La Liga da 104 a Champions League da 23 a Copa del Rey da 13 a Spanish Super Cup da tara a Club World Cup da karawa hudu a Uefa Super Cup.

An yi nasara 291 da shi a wasannin Real Madrid, wanda ya ci mata ƙwallo 28 kawo yanzu.