Lewandowski ya kai Barca mataki na daya a La Liga

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Robert Lewandowski ya ci kwallo biyu ya kai Barcelona mataki na daya a La Liga, bayan doke Elche a ranar Asabar.

Barcelona ta yi nasara da ci 3-0 a wasan mako na shida a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da suka kara a Nou Camp.

Dan wasan tawagar Poland, ya ci ta farko kan hutu da ta uku a zagaye na biyu, yayin da Memphis Depay ya zura na biyu saura minti hudu su je hutu.

Kawo yanzu lewandowski ya ci wa Barcelona kwallo 11 a fafatawa takwas da fara kakar nan.

To sai dai a minti na 14 aka bai wa kyftin din Elche, Gonzalo Verdu jan kati, sakamakon jan Lewandowski da ya yi wanda ke kokarin cin kwallo.

Barcelona ta mamaye wasan gabaki dayansa har da kai hare-hare 25, ita kuwa Elche daya kwal ta yi.

Pedri ma ya ci kwallo amma aka soke, bayan da VAR ta yanke hukunci.

Barcelona ta dare teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Real Madrid, wadda za ta ziyarci Atletico Madrid ranar Lahadi a wasan hamayya.