Yadda 'sakacin' likita ya kumbura hannun jariri a Kano

..
An wallafa

Hukumomi a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sun kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan yadda wani hannun wani jariri ya ke neman lalacewa sanadiyar ɗaurin da aka yi masa.

Hannun jaririn ya kumbura bayan da wani likita ya manta bai cire robar da ya ɗaure hannun ba, lokacin da yake gudanar da wasu gwaje-gwaje.

Iyayen jaririn ɗan kasa da mako daya, sun ce suna bukatar a ba su kulawa ta musamman tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Jami’an asibitin na Malam Aminu Kano sun tabbatar da cewa hannun jaririn ya  kumbura kuma yanzu haka ana masa magani.

Ana zargin likitan da ya kula da jaririn ya bar robar da ya ɗaure hannun jaririn yayin da yake yi masa aiki, har tsawon sa’a goma sha takwas, abin da ya haifar da mummanan kumburin, kuma a lokacin da abin ya faru kwanansa uku da haihuwa.

Shugaban asibitin Farfesa Abdurrahman Abdu Sheshe, ya ce sun kafa kwamitin da zai gudanar da bincike don gano abin da ya faru.

Jihar Kano wadda ke kan gaba wajen yawan al’umma a arewacin Najeriya, bayanai na cewa jama’a da dama na kokawa kan yadda wasu likitoci ke muzguna musu da kuma sakaci da aiki, amma shugaban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Abdu Sheshe ya ce duk marasa lafiya ko dan uwan marasa lafiyar da bai gamsu da yadda ake kula da shi ba to a hanzarta kai koke ga jami’an asibitin don daukar mataki.