Waiwaye: Ƙarin albashi, sauke Ndume da dukan Danbilki Kwamanda

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

..

Asalin hoton, FACEBOOK/ABDULMAJEED ALMUSTAPHA KWAMANDA

Bayanan hoto, Danbilki Kwamanda ya shahara wajen sukar gwamnatoci da 'yansiyasa a arewacin Najeriya

A cikin makon ne kuma wani bidiyo ya ɓulla a shafukan sada zumunta na yadda wasu mutane da ba a san ko su wane ba, ke duka fitaccen ɗan siyasar nan na jihar Kano, Abdulmajid Danbilki da aka fi sani da Danbilki Kwamanda, mai yawan magana a kafofin yaɗa labarai da bulala bayan sun ɗaure hannunsa da ankwa

An ji mutanen da ba a ganin su a bidiyon na tuhumar sa kan dalilin da ya sa "yake zagin" gwamnan Kaduna Uba Sani, yayin da shi kuma yake musanta zargin.

Kwamanda ya shahara wajen sukar gwamnatoci da ƴan siyasa tsawon shekaru a kafofin yaɗa labarai na jihar Kano da wajenta. Yakan soki ƴan adawa da kuma jam'iyyarsa ta APC mai mulkin Najeriya.

Tinubu ya amince da N70,000 mafi ƙanƙantar albashi

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Tinubu/X

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu

A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan gwamnatin ƙasar.

Tinubu ya sanar da sabon albashin ne a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.

Sabon albashin mafi ƙanƙanta da ake sa ran shugaban ƙasa zai gabatar wa Majalisar Dokokin Tarayya shi ne naira 70,000."

Majalisar Dattawa ta tsige Ndume daga muƙaminsa kan sukar shugaban ƙasa

Ndume

Asalin hoton, SENATENG

Bayanan hoto, Sanata Ali Ndume

A ranar Larabar makon ne kuma Majalisar dattiwan Najeriya ta cire sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume daga muƙamin mai tsawatarwa.

Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan ƙorafi da jam'iyyar APC, mai mulki ta yi kan wasu kalaman sanatan a baya-bayan nan.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto wata wasiƙar ƙorafi daga shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma sakatarenta, Sanata Bashir Ajibola.

Abba Kabir ya naɗa sarakuna uku masu daraja ta biyu a Kano

..

Asalin hoton, KNSG

Bayanan hoto, Gwamna ya bai wa sabbin sarakunan takardun kama aiki ranar Talata a fadar gwamnatin Kano

A cikin makon ne kuma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin sarakuna uku masu daraja ta biyu a jihar.

Hakan na zuwa jim kaɗan bayan sanya hannu kan sbauwar dokar da ta amince da ƙirƙirar sabbin masarautu uku masu daraja ta biyu da majalisar dokokin jihar da yi.

Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar ta ce sarakunan da aka amince da naɗa su sun haɗa da Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin sarkin Karaye, da Muhammad Isa Umar, a matsayin sarkin Rano da kuma Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sarkin Gaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa naɗin sabbin sarakunan ya fara aiki nan take.

Gwamnatin Tarayya ta bai wa gwamnoni tirelolin shinkafa don raba wa talakawa

...

Asalin hoton, others

Bayanan hoto, Gwamnatin Tarayya na fatan gwamnonin za su raba shinkafar ga mabuƙata a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

A farkon wannan makon ne kuma gwamnatin Najeriya ta ce ta bai wa kowace jiha haɗi da Abuja tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.

Ministan watsa labaran ƙasar Mohamed Idris ne ya tabbatar da haka bayan kammala taron majalisar zartarwa a ranar Litinin.

Ya ce kowace tirela tana ɗauke da buhun shinkafa 1,200 masu nauyin kilogiram 25 da aka bai wa gwamnonin jihohi a wani mataki na rage wa talakawa raɗaɗin ƙarancin abinci da tsadarsa da ake fuskanta a ƙasar.

Ƴan majalisar wakilai sun sadaukar da rabin albashinsu don rage matsin rayuwa

...

Asalin hoton, NASS

A cikin makon ne kuma 'yan majalisar wakilan Najeriya sun amince da zabtare kashi 50 na albashinsu har na tsawon watanni shida a wani mataki na nuna tausayawa ga yanayin matsin tattalin arziƙi da yunwa da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Hakan na zuwa ne bayan amincewa da gyaran ga buƙatar da mataimakin shugaban majalisa, Benjamin Kalu ya yi na buƙatar ƴan majalisar da su sadaukar da kashi 50 na albashin nasu na naira 600,000 da suke karɓa.

Hon Benjamin Kalu ya ce zabtare albashin nasu zai taimaka wa gwamnati wajen sauƙaƙa wa ƴan ƙasar rayuwarsu.