Mutum 13 sun mutu a Iraki a hare-haren Iran kan Kurdawa

Asalin hoton, EPA
Mutum 13 sun mutu a yankin Kurdistan da ke Iraƙi, a cewar jami'ai, a hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta ƙaddamar a wuraren da ta ce sansanonin ƙungiyoyin hamayya ne na Kurdawan Iran.
Wata mace mai ciki na daga cikin waɗanda rahotanni suka ce ta rasu a hare-haren.
Rundunar sojin juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce harin ya samu "ƴan awaren ƴan ta'adda" da ke goyon bayan boren da ke faruwa a ƙasar.
Zanga-zangar adawa da gwamnati ta karaɗe Iran tun bayan mutuwar wata ƴar ƙabilar Kurɗawa da ke tsare a hannun jami'an tsaro kwana 12 da suka wuce.
Mahsa Amini mai shekara 22 ƴar birnin Saqez da ke arewa maso yammacin ƙasar, ta je ziyara ne Tehran sai yan Hisbah suka kamata bisa zargin ta da taka tsattsaurar doka da ta ce dole mata su dinga saka ɗankwali da sa hijabi.
Ƴan sandan sun ce Ms Amini ta faɗi ne a wajen da ake tsare da ita sakamakon ciwon zuciya.
Amma iyalanta sun yi watsi da wannan dalilin inda suka yi zargin cewa jami'an Hisban ne suka azabtar da ita.
Daga baya ta rasu a asibiti bayan shafe kwana uku a yanayi na dogon suma.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Kurdawa mai suna Hengaw a ranar Litinin ce jami'an tsaro sun kashe Kurdawa masu zanga-zanga 18, aka raunata 898 sannan aka kama fiye da mutum 1,000, a yayin da hukumomin Iran suke ƙoƙarin daƙile boren a yankin da ma wasu wuraren.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ɗin a Iran ta ce yawan masu zanga-zangar da aka kashe ya kai 76, inda kafar yada labaran ƙasar kuma ta ce mutum 41 ne suka rasu, ciki har da jami'an tsaro da mayaƙan sa kai masu goyon bayan gwamnati.
Hukumomin Iran sun ɗora alhakin tarzomar a kan maƙiyan ƙasar da ke wasu ƙasashen da goyon bayan masu zanga-zangar tare da zargin wasu ƙungiyoyin Kurdawan Iran masu ɗauke da makamai da ke ayyukansu a Iraƙi don tayar da husuma a Iran.
A ranar Laraba, Rundunar sojin juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai harin manyan sansanonin da ke Komala, da jam'iyyar Democratic Party of Iranian Kurdistan (PDKI) da kuma Jam'iyyar Kurdistan Freedom Party (PAK), a karo na uku cikin kwana huɗu.
Rundunar ta yi gargaɗin cewa za a ci gaba da kai hare-haren har sai an ɗauki matakin kawar da barazanar.
Komala ya tabbatar da cewa an harba jirage marasa matuƙa 10a yankin Zargwez, PAK ta ce abin ya shafi hedikwatarta da ke Sherawa, sannan PDKI ma ta ce harin ya shafi sansanoninta da hedikwatarta a Koy Sanjaq.
Gwamnatin Yanki ta Kurdawa a wata sanarwa ta ce "Hare-haren makamai masu linzami na Iran a kan duk wasu ƙungiyoyin hamayya bisa kowane irin uzuri abu ne da bai dace ba."
Ita ma gwamnatin tarayyar Iran ta yi Allah-wadai da hare0haren, yayin da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke ƙsar ya gargadi Iran cewa "harin roka rashin hankali ne da ka iya damalmala al'amura."
Amurka ta ce ba zai yiwu Iran ta ɗora alhakin matsalolinta na cikin gida kan maƙwabtan da babu ruwansu ba."
Su waye Kurdawa?
Akwai Kurdawa tsakanin miliyan 25 zuwa 35 da ke zaune a wani yanki mai tsaunuka a kan iyakokin Turkiyya da Iraƙi da Syriya da Iran da kuma Armenia.
Su ne ƙabila ta huɗu mafi girma a yankin Gabas ta Tsakita, amma ba su taɓa samun ƙasa tasu ta kansu ba.
Kusan kashi 10 cikin 100 na Musulmai mabiya mazahabar Shi'a mafiya rinjaye miliyan 84 na Iran, Kurdawa ne, sauran kason duk ƴan Sunni ne da ke zaune a yankuna masu tsaunuka a arewa maso yammacin iyakokin Turkiyya da Iraƙi.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International ta ce Kurdawa ƴan Iran sun sha fuskantar wariya kuma ana danne musu ƴancinsu na zamantakewa da siyasa da tattalin arziki.
Ƙungiyoyin hamayya na Kurdawa da ke samun mafaka a wasu wuraren, wadanda ke neman ƙasarsu ko cin gashin kai a yankinsu, suna yawan yin rikici da dakarun tsaron Iran daga sansanoninsu a yankin Kurdistan da ke Iraƙi.











