Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea na son Toney, PSG na nazari kan Martinez da Osimhen
Chelsea na son ɗanwasan gaba na Brentford da Ingila Ivan Toney, mai shekara 27 da kuma na Brighton da da Jamhuriyyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 19, saboda ɗanwasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25, Paris St-Germain na son ɗaukarsa. (Standard)
Paris St-Germain na sa ido kan ɗanwawasan gaba na Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 26, da ɗanwasan gaba na AC Milan da Portugal Rafael Leao, mai shekara 24, da Osimhen domin maye gurbin ɗanwasanta na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 25, da zai tafi a ƙarshen kaka. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
PSG na kuma son cike giɓin da Mbappe zai haifar inda ƙungiyar ke son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 26, da kuma ɗanwasan tsakiya na Manchester City da Portugal Bernardo Silva, 29. (L'Equipe - in French)
Liverpool na son ɗauko matashin ɗanwasan tsakiya na Leeds United da Ingila mai shekara 17 Archie Gray, yayin da dole Leeds ta sayar da shi idan ba ta ci gaba da buga gasar Firimiya ba. (Football Insider)
Arsenal na sa ido kan Pedro Neto da darajarsa ta kai fam miliyan 60, inda Wolves ta nace kan farashinsa ɗanwasan gaban na Portugal mai shekara 23 wanda Tottenham da Liverpool ke sha’awa. (Standard)
Tsohon ɗanwasan gaba na Liverpool da Uruguay Luis Suarez, mai shekara 37, ya ce Inter Miami da ke buga gasar Major League Soccer ta Amurka zai yi ritaya. (AS)
Ɗanwasan gaba na Sunderland da Ingila Jack Clarke, mai shekara 23, zai bar ƙungiyar kamar yadda wakilinsa ya bayyana bayan da ƙungiyar ta yi watsi da tayin Lazio a Janairu. (Sunderland Echo)
Roma na son sayen ɗanwasan Leeds United da Spain Diego Llorente, mai shekara 30, bayan ya yi bajinta a matsayin ɗanwasan aro. (Yorkshire Evening Post)
Juventus ta gana da tsohon ɗanwasan West Ham Felipe Anderson, yayin da kwangilar ɗanwasan mai shekara 30 za ta kawo ƙarshe a bazara da Lazio. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Kocin Newcastle Eddie Howe ya nuna damuwa cewa daraktan wasannin ƙungiyar Dan Ashworth zai iya fallasa sirin sayen ƴanwasa ga Manchester United, idan har ya koma Old Trafford. (Telegraph - subscription required)