PSG na son Osimhen, darajar Saka ta kai fam miliyan 200 a Arsenal

An wallafa

Ɗanwasan gaba na Napoli da Najeriya striker Victor Osimhen, mai shekara 25, shi ne kan gaba cikin ƴanwasan da Paris St-Germain ke hari domin maye gurbin ɗanwasan gaba na Faransa mai shekara 25 Kylian Mbappe, bayan ya shaida wa ƙungiyar cewa zai raba gari da ita a ƙarshen kaka. (Athletic - subscription required)

Bayern Munich na son raba gari da kocinta Thomas Tuchel a bazara kuma tana son hamayya da Liverpool kan kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso. (Times - subscription required)

Tsohon kocin Jamus da Bayern Munich Hansi Flick na cikin waɗanda Barcelona ke tunanin ɗauka domin maye gurbin Xavi, yayin da Bayern Munich ke tunanin ɗauko kocin mai shekara 58 idan ta kori Tuchel. (Bild)

Tsohon kocin Eintracht Frankfurt Oliver Glasner ya amince ya karɓi ragamar tafiyar da Crystal Palace, da ke shirin sallamar Roy Hodgson. (Times - subscription required)

Brighton na shirin rabuwa da kocinta Roberto de Zerbi a karshen kaka, yayin da Liverpool da Manchester United ke son ɗauko kocin. (Mail)

Ɗanwasan tsakiya na Barcelona da Spain Gavi, mai shekara 19, na cikin ƴanwasan da Paris St-Germain ke hari a bazara. (Athletic - subscription required)

Barcelona na sa ido kan ɗanwasan Arsenal da Brazil Gabriel Martinelli, kuma tana sa ido kan ɗanwasan Brighton da Japan Kaoru Mitoma, mai shekara 26, da kuma na Napoli mai shekara 23 Khvicha Kvaratskhelia, na Georgia. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Arsenal ta kimanta darajar ɗanwasan Ingila mai shekara 22 Bukayo Saka kan fam miliiyan 150 zuwa 200. (Football Insider)

Chelsea da Arsenal na ribibin ɗanwasan tsakiya na West Ham da Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 23. (Fichajes - in Spanish)

Norwich City na son maye kocinta David Wagner da mataimakin kocin Arsenal Carlos Cuesta, a bazara. (Guardian)