Man Utd na sa ido kan Olise, Barca na son ɗauko Amadou Onana

An wallafa

Wolves za ta sayar da Pedro Neto a wannan bazara don kaucewa saɓa dokar kuɗi tare da ba kocin ƙungiyar Gary O'Neil kuɗi ya yi cefane inda kuma Liverpool, Arsenal, Tottenham da Manchester United suka nuna sha'awar ɗanwasan na Portugal mai shekara 23. (Sun)

Manchester United na sa ran cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗauko Dan Ashworth a matsayin darakta a farkon shekara. (Mail)

Newcastle za ta karɓi ƙarin fam miliyan 6 idan har Ashworth ya koma Manchester United. (The i - subscription required)

Manchester United na sa ido kan ɗanwasan Crystal Palace mai shekara 22 Michael Olise. (90min)

Manchester United na son sayen ɗanwasan baya na Brazil Gleison Bremer, mai shekara 26, daga Juventus a bazara. (Calciomercato - in Italian)

Barcelona na burin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Everton da Belgium Amadou Onana mai shekara 22. (Fichajes - in Spanish)

Tsohon kocin Brighton da Chelsea Graham Potter zai iya maye gurbin David Moyes idan ya bar West Ham a karshen kaka. (Telegraph - subscription required)

Manchester City na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na West Ham da Brazil Lucas Paqueta, mai shekara 26. (Football Insider)

Manchester City da Liverpool na cikin sahun ƙungiyoyin da ke son ɗanwasan tsakiya na Shakhtar Donetsk da Ukraine Georgiy Sudakov, mai shekara 21. (Calciomercato - in Italian)

Barcelona na sa ido kan ƴarwasan gaba ta Ingila Lauren Hemp yayin da kwangilarta za ta kawo ƙarshe a barazana a Manchester City. (Standard)

Barcelona na son fam miliyan 85 kan ɗanwasan tsakiya na Netherlands Frenkie de Jong mai shekara 26, wanda ake alaƙantawa da Manchester United da kuma Chelsea. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Crystal Palace na tunanin ɗauko tsohon kocin Eintracht Frankfurt Oliver Glasner idan har ta raba gari da Roy Hodgson. (Guardian)

Everton da Crystal Palace na sa ido kan ɗanwasan gaba na Marseille mai shekara 23 na Senegal Iliman Ndiaye. (La Provence via Sport Witness)