Newcastle ta amince daraktan wasanta ya koma Manchester United

An wallafa

Daraktan wasan Newcastle Unite, Dan Ashworth zai koma Manchester United da aiki, bayan da ya sanar da kungiyar St James Park yana son motsawa.

United na fatan ta koma kan ganiya tun bayan da Ineos ya mallaki hannun jarin kungiyar kaso mafi tsoka.

Sai dai har yanzu ba a fayyace ko an fara tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu kan batun daukar Ashworth ba.

Ashworth yana da yarjejeniya da Newcastle zuwa 2025, wadda ta hana mai shekara 52 aiki a wani wajen har sai an cimma biyan wani lada, idan kwantiraginsa bai kare ba.

Watakila Newcastle ta bukaci United ta biya £10m, wato sauuran kunshin yarjejeniyar da ta rage da Ashworth.

Ana kwatanta Ashworth a matakin daraktan wasanni mafi kwarewa a fannin tamaula, ana cewa yana da hannu da Newcastle ta dauko Sandro Tonali daga AC Milan kan £55m a watan Yuni.

Sai dai wasa 12 Tonali ya buga wa Newcastle daga baya aka dakatar da shi wata 10, bayan da aka same shi da laifin karya ƙa'idar yin caca.

Ashworth ya taka rawar gani a tawagar Ingila ta matasa, wadda ta lashe kofin duniya na ƴan shekara 17 da kuma ƴan shekara 20.

Shi ne ya tsara yadda Brighton ta taka rawar gani har shiga Premier League da daukar Graham Potter, bayan da aka kori Chris Hughton.

Daga nan ne Ashworth ya koma Newcastle United a 2022.