Ku San Malamanku tare da Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa, malamin da ya yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar

A wannan makon filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Malam Abubakar Ashafa da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.
Malamin ya shaida wa BBC Hausa cewa an haife a unguwar Madatai da ke tsakiyar birnin Kano, a shekarar 1974.
Malam Abubakar ya soma karatunsa na allo a gida - wato a makarantar Islamiyya da ke gidansu, tun daga farkon rubutu har zuwa sauke Alkur’ani.
Malam Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa, mutumin Gaya ne ta jihar Kano, kakansa Malam Muhammadu na Tanda ne ya shiga garin Kano, inda ya assasa makarantar Islamiyya da ya sanya wa suna Tandawiyya Islamiyya kuma har yanzu ana koyarwar ilimin addini a wannan makaranta.
Ya ce daga nan ne mahaifinsa ya kai shi wurin abokansa malamai domin daukar karatu da kara gogewa, ciki har da aminin mahaifinsa Malam Isyaka kan Tudu.
Baya ga wannan mahaifinsa ya mika shi ga wani fitaccen malami mai suna Malam Aminu Sanda inda nan ma ya yi karatu mai zurfi.
Malamin ya yi karatu a wurin mashahuran malamai a Kano, ciki har da su Malam Musa Gabari, da Malam Dan Tsoho Madabo da sauransu. Malamin ya kware a fannin Fiqihu inda har ya yi rubuce-rubuce kan hakan.
Malam Abubakar Ashafa ya yi karatun firamare a makarantar Tudun Madatai, daga 1980 zuwa 1987.
Daga nan ya tafi makarantar Sakandare ta Aliya, amma bangaren Arabiyya, a shekarar 1993 ya kammala karatun babbar sakandare.
Tun daga wancan lokacin bai kara yunkurin shiga wata makaranta a gaba ko da kuwa jami’a ce ba, amma a shekarar 2006 ya yi nasarar shiga Jami’ar Bayero inda ya karanci fannin ilimi wato Education.
Iyaye da kakannin Malam Abubakar sun yi fice a fannin karatun Ashafa, daya daga cikin dalilan da suka sanya ake yi musu lakabi da Mai Ashafa.
Kamar yadda al’ada take a birnin Kano, kowacce unguwa akwai abin da suka yi fice a kai, ko dai a fannin ilimi ko kasuwanci da sauransu.
Misali kowa ya san unguwar Madabo ta yi fice da malaman ilimin Fiqihu ne, Chiroma gidan Hadisi, wannan dalili ya sanya aka yi wa gidan Malam Amadu da gidan Ashafa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya yi karatun littafan addinin tun daga Kawa‘idi, da Risala, da Ishimawi, da Azkari, har zuwa Iziyya.
"Daya daga cikin kalubalen da na fara fuskanta a fannin ilimi ya fara ne lokacin da na shiga jami’a, sakamakon zabar fannin Education da na yi, kusan dukkan karatun da na yi kafin wannan lokacin da Larabci na yi, don haka da na zo jami’a sai komai ya sauya," in ji Malam Abubakar.
Ya ci gaba da cewa: "Ba na mantawa ranar farko da muka fara daukar karatu, sai na ji malamin na ta zuba turanci, kusan ban fahimci komai da yake magana akai ba.
"Abin da ya fara zuwa raina shi ne lamarin nan ko dai a yi ne ko kuma na fasa, Allah ya taimake ni a can layi karshe nake, duk mutanen da malamin ke tashi domin amsa tambayoyi babu ni a ciki."
Malam Abubakar ya ce daga nan ya lura da wanda ya fi kowa zakewa wajen amsa tambaya, yana mai cewa "ai ana fitowa sai na same shi na shaida masa babu abin da na gane a karatun nan baki daya. Ina son ka taimaka min idan na wuce wannan lokacin ba tare da na yi wani abu ba, gaskiya sai dai na hakura da karatun.’’
Haka dai aka yi ta fafatawa har Allah ya kai malamin kammala digiri na farko, ya yi dirigi na biyu, har ga shi a halin yanzu yana kokarin yin digirin digirgir.
'Muqabala da Sheikh Abduljabbar'
Malam Abubakar ya ce ya shiga sahun masu mukabala da malamin nan mai jawo ce-ce-ku-ce Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ne saboda ya ga yana sukar manzon Allah (SAW).
Ya ce da fari malamai irin sa suna yabon malamin saboda yanayin koyarwa da karatukansa.
Amma daga bisani da lamarin ya sauya dole suka ja daga lokacin da ya fara ketare wasu iyakoki "ya fara tabo sahabban Manzon Allah (SAW) da ma shi kansa annabin Allah".
Daya daga cikin dalilan da suka sanya Malam Abubakar ya ce ya yi rubutu kenan, lokacin Malam Abduljabbar ya "fara daga yatsa ga sahabban Manzon Allah SAW, na yi masa raddi a littafina mai shafi kusan 100."
Ya ce: "Malam Abduljabbar ya yi ta kuri cewa cikin kwana guda zai mayar da martani kan rubutun amma hakan ba ta yiwu ba, sannan ya sha yin kuri a zo a yi mukabalar amma abu ya gagara.
Da tafiya ta yi nisa, ya fara kaucewa hanya bayan sanyo Manzon Allah SAW ne aka taru aka yi wannan mukakabala, kuma tana daya daga cikin abin da nake alfahari da su."
Iyali
Malam Abubakar ya ce yana da mace guda da ‘ya’ya har da jika daya.
Abinci
Malamin ya ce yana cin kowanne irin abinci amma babu kamar wake da shinkafa da yaji. Ya kara da cewa shi ma’abocin shan shayi ne.










