Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa muke toshe hanyoyin manyan wurare a Najeriya – Ƙungiyar ɗalibai
Daliban jami’o’in Najeriya na ci gaba da zanga-zangar lumana a sassan ƙasar daban-daban.
Ko a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ɗaliban sun toshe hanyar shiga filin jirgin sama na Murtala Muhammad tare da wasu manyan hanyoyi, wani lamari da ya haifar da cikas ga sufurin jiragen.
Hakan dai wani ƙoƙari ne da suke yi domin matsawa gwamnatin ƙasar lamba don ta magance yajin aikin da malaman jami’o’in Najeriya ke ci gaba da yi, sama da wata shida.
Daliban sun ce a ranar Talata za su toshe hanyoyin da za su kai ga babbar tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, da kuma babban kamfanin man fetur na NNPC da ke babban birnin ƙasar, Abuja.
Shugaban ƙungiyar ɗaliban jamio’i na ƙasar Comrade Umar Faruk Lawan, ya shaida wa BBC cewa daga cikin dalilinsu na yin zanga-zangar shi ne don jawo hankalin gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace a kan yajin aikin da aka shafe watanni ana yi.
“Idan aka duba kalanda yau wajen wata takwas kenan ana yajin aiki a jami’o’in Najeriya gaba ɗaya. Idan ba mu yi zanga-zangar ba har aka fara tafiyar siyasa a ranar 28 ga watan Satumban nan, to gaskiya babu wanda zai saurari ɗalibai.
“Za su ci gaba da harkar siyasarsu ne, sai an gama siyasa sannan za su waiwayi ɗalibai,” in ji shi.
Ya jaddada cewa shi ya sa suke wannan tattaki don jawo hankalin gwamnati ta saurari batun ɗalibai.
“Mun so mu yi a Abuja ma amma ana ta ba mu haƙuri da la’akari da matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar. Shi ya sa muka haƙura da yi a can. Amma muna nan muna shiri, za mu iya yi da kowane lokaci.”
Ya ce suna toshe hanyoyin manyan wurare na ƙasar ne saboda hakan ne kawai zai jawo hankalin hukumomi kan abin da suke yi har a saurare su .
“Idan ba mu yi haka ba babu mai sauraronmu,” ya ce.
Sai dai mutane da dama masu fafurukar neman abin rufin asiri sun koka cewa wannan toshe hanyoyi na yin mummunan tasiri kan harkokinsu na yau da kullum.
Amma Kwamared Umar Faruk ya ce masu kuɗi da masu mulki lamarin ya fi shafa, kuma dama su ne ake son jawo hankalinsu kan batun.
“Muma abin ya fi shafa ai, wata bakwai zuwa takwas babu karatu,” ya ce.
Shugaban daliban ya ƙara da cewa ya yi amanna ba gwamnati ce kadai mai laifi a batun yajin aikin ba, ita ma ƙungiyar malamai ta ASUU da nata laifin.
“Shi ya sa ma mako biyu da suka wuce na kai gwamnati da ita ASUU ƙara kotu, saboda hakan zai sa dole su zo a zauna a cimma matsaya,” a cewar Kwamared.
Ya ƙara da cewa a yanzun ma ba su fitar da tsammanin cewa kafin makon nan ya ƙare za a cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu ba.
Kafin su ɗauki matakin toshe hanyoyin manyan wurare da kuma zuwa kotu, Kwamared ya ce sai da suka yi ƙoƙarin ganawa da gwamnati da kuma ASUU, amma hakan ya ci tura.
To ko me ƙungiyar NANS ke so gwamnati ta yi wa ɗaliban don samun salama?
Shugaban ɗaliban ya ce “wannan tsakanin gwamnati ne da ASUU, don sun ma ƙi gaya mana abin da yake tsakaninsu.
“Sai dai bincikenmu ya nuna mana cewa gwamnati ta ce za ta ba su wasu kuɗaɗe amma ASUU ta ce kuɗaden sun musu kaɗan.
“Mu yanzu abin da muke so shi ne ita ASUU ta duba ta yi haƙuri tun da ba lallai ka samu yadda kake so duka ba.”
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Me ƴan Najeriya ke cewa kan zanga-zangar?
Wannan batu na zanga-zangar ɗaliban jami’ar na daga wadanda aka fi tattaunawa a kansu a shafukan sada zumunta a Najeriya.
An ƙaddamar da maudu’i mai taken #NANS, inda aka yi amfani da shi sau kusan 18,000 zuwa yammacin ranar Talata.
Wasu na yabon ƙungiyar ɗaliban ne kan yadda take nuna damuwa da yajin aikin da ake yi, yayin da wasu kuma sukarta suke yi kan salon da take bi ɗin.
Ga dai abin da wasu ke cewa:
Dr Dípò Awójídé @OgbeniDipo ya ce "Kwana biyu da suka wuce shugaban ƙsa ya yi tafiya ta filin jirgi. Mataimakin shugaban ƙasa ma ya yi amfani da filin jirgin kwana biyu da suka wuce. Ƙungiyar ɗalibai ta NANS ba ta toshe su ba. Me ya sa abin sai a kan talakan da bai ji ba bai gani ba zai ƙare, bayan dama su da ƴan uwansu na cikin halin ƙaƙa-i-kayin? Gaskiya wannan bai dace ba.
Nze. Amamba@nnamdiiaya rubuta cewa "NANS ta tsara zanga-zangar nan ta yau sosai. Idan har kowa yana ƙorafi, to lallai a kan daidai suke. Da yawanku kuna son ganin sabuwar Najeriya ba tare da yin wata hoɓɓasa ba, sannan ba ku shirya jurewa abin da hakan ka iya zuwa da shi ba but you are not ready to pay a little inconvenience for it. That's why you come online to yap about bad governance only to
Sanata Shehu Sani@ShehuSani ya ce "Bai kamata NANS ta toshe babbar hanyar Lagos-Ibadan ba. Ba ita manyan masu faɗa a hin ke bi ba."