Pochettino ba zai yadda da zalamar son buga fenariti ba a Chelsea

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Chelsea, Mauricio Pochettino ya ce bai ji dadi ba kan takaddamar wanda zai buga fenariti a wasan da suka caskara Everton 6-0 a Premier League ranar Litinin.

Ya kuma ja kunnen 'yan wasa da kada su kara nuna hakan a wasannin Chelsea nan gaba, domin zubar da kimar kunciyar ce.

Nicolas Jackson da Noni Madueke sun yi takaddamar wanda zai buga fenariti, kafin daga baya Cole Palmer ya karba ya buga ya kuma ci kwallon.

"Ba zan amince da irin wannan halayyar ba," in ji Pochettino.

"Na kuma sanar da su cewar wannan ne na karshe da hakan zai sake faruwa.''

Ya kara da cewar bai kamata a samu irin takaddama haka ba, bayan kwazon da kungiyar ta yi a kan Everton.

A minti na 64 Palmer ya ci fenaritin - na tara da ya buga kuma ya ci a Chelsea a kakar nan.

Tun farko Madueke da Jackson suka yi ta takaddamar wanda zai buga fenaritin, bayan da suka karbi kwallo a wajen Malo Gusto, inda Madueke ya fara zuwa wajen.

Daga baya Thiago Silva ya sa baki sai Jackson ya hakura da buga fenaritin, bayan kusan dakika 30 suna cacar baki a tsakaninsu.

Sai kuma kyaftin, Conor Gallagher ya je wajen Madueke ya nuna Palmer ya ce ya bar masa kwallon ya buga.

Madueke bai amince ba daga baya Gallagher ya karbe kwallon ya bai wa Palmer.

Daga baya Jackson ya koma wajen buga fenaritin, inda Palmer da Gallager suka ture shi sai kuma Gallagher ya ture Madueke, hakan ya bai wa Palmer damar buga fenaritin.

Pochettino ya ce kowa a Chelsea ya kwan da sanin cewar Palmer ne mai buga wa kungiyar dukan bugun daga kai sai mai tsaron raga.