Ansu Fati ya ji rauni a wajen atisaye a Barcelona

Ansu Fati

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Barcelona, Ansu Fati ya ji rauni a wajen atisayen ƙungiyar ranar Laraba.

Sakamakon raunin da Fati ya ji, ana cewar watakila zai yi jinyar mako huɗu, kafin ya koma fagen daga.

Sauran ƴan wasan Barcelona sun ci gaba da atisaye a cikin ruwa a Ciutat Esportiva, bayan da aka gayyaci wasu manyan ƴan ƙungiyar, domin buga wa kasashensu tamaula.

Fati ya ci karo da koma baya a wasannin bana, sakamakon raunin da ya ji, wanda zai yi jinya tare da wasu daga ƴan ƙungiyar har da Lamine Yamal da Robert Lewandowski.

Fati ya shiga cikin ƴan wasan Barcelona yana da shekara 17 a 2019, daga baya ya karɓi lamba 10 rigar da Lionel Messi ya ajiye, bayan da ya koma Paris St Germain.

Ɗan wasan ya yi fama da jinya a Nuwambar 2020, hakan ya sa ya kasa komawa kan ganiya.

Bai yi wasa 14 ba a kakar 2023/24 a Brighton & Hove Albion mai buga Premier League, wadda ya yi wa karawar aro a bara.

Fati ɗan wasan tawagar Sifaniya, ya buga karawa bakwai a Barcelona a dukkan fafatawa a bana, inda aka fara wasa ɗaya da shi daga ciki.

Barcelona, wadda take ta ɗaya a kan teburin La Liga da tazarar maki shida tsakani da Real Madrid, za ta je Celta Vigo a karawar gaba ranar 223 ga watan Nuwamba.