Tottenham na zawarcin Danso da Disasi, Crystal Palace ta tuntuɓi Chelsea kan Chilwell

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Da alama Tottenham Hotspur ta kere wa Wolves a fafutukar sayen ɗanwasan Lens kuma mai tsaron bayan Austria Kevin Danso mai shekara 26. (Talksport).

Kazalika Tottenham ɗin ta bayyana sha'awar sayen ɗanwasan Chelsea ɗan asalin Faransa Axel Disasi mai shekara 26, ko da ƙoƙarin sayen ɗanwasan Ingila Fikayo Tomori mai shekara 27 daga AC Milan ya ci tura. (Telegraph).

Mai tsaron bayan Newcastle ɗan asalin Ingila Lloyd Kelly, 26, na dab da komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus. (Chronicle).

Southampton na zawarcin ɗan wasan Ivory Coast Loubadhe Abakar Sylla, 22 daga ƙungiyar Strasbourg a kan aro. (Fabrizio Romano).

Crystal Palace kuwa ta tuntuɓi Chelsea game da sayen ɗanwasan bayan Ingila Ben Chilwell, 28, a matsayin aro. (Athletic - subscription required).

Shirin aron ɗanwasan Manchester United Tyrell Malacia zuwa Benfica ya ruguje sai dai har yanzu ɗanwasan mai shekara 25 na iya barin Man Utd a kasuwar musayar ƴanwasa. (Fabrizio Romano).

United ɗin kuma ta ƙara ƙaimi a zawarcin ɗanwasan gaban Mali El Bilal Toure, 23, wanda a yanzu haka yake zaman aro a Stuttgart daga Atalanta. (Teamtalk).

AC Milan ta kusa ɗaukan Santiago Gimenez, 23 ɗanwasan Feyenoord da Mexico.(Goal).

West Ham ta yi tayin kusan fam miliyan 30 don sayen fitaccen ɗanwasan Faransa mai shekara 18 Eli Junior Kroupi wanda yanzu haka yake tare da Lorient. (Football Insider).

Burnley kuwa ta kusa sayen ɗanwasan Ingila Marcus Edwards mai shekara 26 daga Sporting. (Talksport).

Middlesbrough na tattaunawa da Aston Villa don sayen ɗanwasanta Samuel Iling-Junior, 21, da yake zaman aro a Bologna. (Mail).

Napoli na shirin kammala ɗaukan aron ɗanwasan Faransa Allan Saint-Maximin, 27, da yake zaman aro a Fenerbahce daga ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya. (Calciomercato).

Marseille na son ɗaukar aron ɗanwasan bayan Chelsea ɗan ƙasar Argentina Aaron Anselmino, mai shekara 19. (Footmercato - in French).

Yunƙurin da Bayern Munich ta yi na sayen ɗanwasan gaban Chelsea ɗan ƙasar Faransa, Christopher Nkunku, mai shekara 27, ba zai tabbata ba a kasuwar musayar 'yan wasa ta yanzu amma za a iya tada batun a bazara. (Kirista Falk).