Salah ya ci Bournemouth ƙwallo biyu a Premier League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta ci gaba da zama ta ɗaya da tazarar maki tara a teburin Premier League, bayan da Mohamed Salah ya ci Bournemouth ƙwallo biyu a filin Vitality.

Kawo yanzu Salah ya ci ƙwallo 178 a lik, ya zama na shida a jerin waɗanda suka ci ƙwallaye da yawa a tarihin Premier League, ya shiga gaban Frank Lampard mai 177.

Ɗan kasar Masar ya fara ci wa Liverpool ƙwallo a wasan mako na 24 ranar Asabar a minti na 30 a bugun fenariti, bayan da Lewis Cook ya yi wa Cody Gakpo keta cikin da'ira ta 18.

Bournemouth na taka rawar gani a kakar nan, wadda ta fuskanci Liverpool, bayan wasa 11 a Premier League ba tare da an doke ta ba.

A kakar nan ta yi nasara a kan Arsenal da Manchester City da Nottingham daga cikin manyan ƙungiyoyin da suka sha kashi a hannunta.

Da wannan sakamakon Liverpool ta haɗa maki 56 daga karawa 23 da kwantan wasa da Everton.

Arsenal za ta iya rage tazarar maki tsakaninta da Liverpool da zarar ta doke Manchester City ranar Lahadi a Emirates.

Wasannin Liverpool uku nan gaba:

League Cup Ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu

  • Liverpool da Tottenha

English FA Cup Ranar Lahadi 9 ga watan Fabrairu

  • Plymouth da Liverpool

English Premier Ranar Laraba 12 ga watan Fabrairu

  • Everton da Liverpool