Yadda Liverpool da Tottenham za su kece raini a Carabao

Ange Postecoglou  da Arne Slot

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A ranar Alhamis ɗin nan ne Liverpool da Tottenham za su yi karo na biyu na wasan kusa da karshe na cin Kofin Carabao, inda masu horad da ƙungiyoyin biyu kowa ke harin kaiwa wasan ƙarshe na farko a tarihinsu a ƙwallon ƙafar Ingila.

Tottenham -wadda ta ci wannan kofi (EFL) shekara 17 baya, ta yi nasara a karawarsu ta farko a gidanta inda ta doke Liverpool da ci 1-0 , mako hɗu da ya gabata.

Kociyan Tottenham Ange Postecoglou na cikin matsi inda ƙungiyar tasa ke fama da jiyyar 'yanwasa kuma take ta 14 a cikin ƙungiyoyi 20 a teburin Premier.

Ita kuwa Liverpool, da ke riƙe da Kofin tauraruwarta na haskawa a ƙarƙashin kociyanta Arne Slot, inda take ta ɗaya a teburin na Premier da tazarar maki shida da kuma kwantan wasa ɗaya, sannan kuma tana kan hanyarta ta shiga matakin ƙungiyoyi 16 a gasar Zakarun Turai.

Duk ƙungiyar da ta yi nasara a wasan za ta fuskanci Newcastle, wadda ta yi waje da Arsenal, a filin wasa na Wembley ranar Lahadi, 16 ga watan Maris.

Kociyan Liverpool Slot ya ce ɗanbayansa na gefen dama Trent Alexander-Arnold ba zai yi wasan ba saboda jinya.

An canza ɗanwasan na Ingila ne a minti na 70 a wasansu na Premier da suka doke Bournemouth ranar Asabar, inda ake ganin ya ji ciwo a cinya.

Wasan gaba na Liverpool ɗin zai kasance ne da ƙungiyar Plymouth ta gasar ƙasa da Premier wato Championship a wasan Kofin FA zagaye na huɗu ranar Lahadi.