Tottenham za ta yi tayin da ba a taba ganin irinsa ba kan Semenyo, Chelsea na zawarcin Smit

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gefe na Tottenham Brennan Johnson na cikin jerin yan wasan da Crystal Palace ke son ta dauka a watan Janairu, saboda tana son dan wasan tawagar kwallon kafa na yankin Wales mai shekara 24 ya taimaka mata wajen cimma burinta na samun shiga gasar Zakarun Turai. (Telegraph)
Tottenham ta shirya yin tayin da ba a taba ganin irinsa ba don sayen dan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25. Kungiyar za ta biya kudi n da ya fi abin da ta tanada a kan dan wasan domin ta sha gaban Manchester City da Liverpool wadanda ke sha'awar daukansa.(Teamtalk)
Chelsea ce a kan gaba a jerin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiya na AZ Alkmaar da kuma Netherlands Kees Smit, mai shekara 19, wanda Newcastle da Manchester United da kuma Tottenham ke zawarcinsa. (The I )
Sha'awar da Newcastle ta nuna kan wasan baya na Toulouse da Faransa Dayann Methalie,mai shekara 19, ka iya kawo karshen tamaular dan wasan Switzerland Fabian Schar mai shekara 33 a kungiyar saboda kwantariginsa zai kare a bazara mai zuwa (Football Insider)
Dan wasa mai kai hari na West Ham Niclas Fullkrug na cikin wadanda AC Milan ke son ta dauka a watan Janairu yayin da dan wasan Jamus mai shekara 32 ke son ya bar kungiyar. (Gazzetta dello Sport)
Crystal Palace ta kosa ta dauki dan wasan Bayern Munich Sacha Boey, mai shekara 25, wanda ake sa ran zai bar Bundesliga a watan Janairu. (Fabrizio Romano)
Kawo yanzu West Ham da Lazio da AC Milan na zawarcin dan wasan Italiya da Sassuolo Andrea Pinamonti mai shekara 26.(Calciomercato )
Dan wasan tsakiya na Everton James Garner mai shekara 24 ya dau hankalin Nottingham Forest duk da cewa abu ne mai wuya ya bar kungiyar a watan Janairu saboda yana wasa akai-akai aToffees. (Mail)
Chelsea da Manchester United sun kara kaimi wajen zwarcin dan wasan tsakiya na Sunderland da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Noah Sadiki, mai shekara 20, bayan ya fara tamaula da kafar dama a Ingila .(Football Insider)













