Yamal ya lashe ƙyautar gwarzon matashin ɗan ƙwallon 2024

Lamin Yamal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan tawagar Sifaniya da Barcelona, Lamine Yamal ya lashe ƙyautar gwarzon matashin ɗan ƙwallon 2024.

Jaridar Italiya, Tuttosport ce ke shirya bikin, wadda ke karrama fitatcen matashin ɗan wasan nahiyar Turai, mai shekara kasa da 24 da ya yi fice a taka leda a kakar tamaula.

Yamal, mai shekara 17 ya nuna kansa a bara a Barcelona, wanda yake buga mata tamaula a koda yaushe, ya lashe Euro 2024 a Sifaniya a gasar Jamus a bana.

Ya ci ƙwallo ya kuma bayar da huɗu aka zura a raga, wanda aka bai wa ƙyautar gwarzon ɗan wasan gasar ta cin kofin nahiyar Turai.

Cikin wattan Oktoba, Yamal ya karɓi lambar yabo ta Kopa Trophy, mai daraja irin ta Ballon d'Or da aka yi bikin a bana.

Yamal ya ci ƙwallo shida ya bayar da takwas aka zura a raga a karawa 16 a dukkan fafatawa a kakar nan.

Ɗan wasan tawagar Ingila da Real Madrid, Jude Bellingham shi ne ya lashe kyautar gwarzon matashin ɗan wasa a 2023.