Potter ya fara da nasara a wasan farko a Stamford Bridge a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta doke Wolverhampton 3-0 a gasar Premier League da suka fafata ranar Asabar a Stamford Bridge.
Wadanda suka ci wa Chelsea kwallayen sun hada da Kai Havertz da Christian Pulisic da kuma Armando Broja.
Kenan Havertz ya ci kwallo na 50 a tarihin sana'arsa ta murza leda, mai 36 a Bundesliga da 14 a Premier League.
Wannan shi ne wasan farko da Graham Potter ya ja ragamar Chelsea a Stamford Bridge a Premier League.
Tsohon kociyan Brighton ya maye gurbin Thmosa Thucel, wanda Chelsea ta kora a bana, bayan da ya kasa taka rawar gani.
Kawo yanzu Potter ya ja ragamar wasa hudu da cin uku da canjaras daya, har da cin Milan 3-0 a Champions League.
Wolves ta buga wasan a karon farko, bayan da ta sallami kociyanta Bruno Lage.
Haka kuma Diego Costa ya buga wa Wolves wasan, inda ya fuskanci tsohuwar kungiyarsa.
Costa ya ci kwallo 52 a wasa 89 da ya yi wa kungiyar Stamford Bridge daga 2014 zuwa 2019.











