Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Carvalho ya koma buga wasannin aro a Hull City
An wallafa
Hull City mai buga Championship ta dauki aron dan kwallon Liverpool, Fabio Carvalho zuwa karshen kakar bana.
Mai shekara 21 dan kwallon tawagar Portugal, ya buga wasannin aro a RB Leipzig kaka daya da rabi - amma sau daya ya buga wa kungiyar ta Jamus tamaula.
Carvalho ya fara taka leda a Fulham da cin kwallo 11 a wasa 40 a lik daga baya ya koma Liverpool kan £5m a Yulin 2022.
Zai fara buga wa Hull City wasa daga ranar Juma'a a karawar da za ta karbi bakuncin Norwich City.
Kociyan Hull City, Liam Rosenior ya ce daukar Carvalho da ya yi, zai taimakawa kungiyar a wasannin da take buga wa a bana.