Abubuwa biyar da suka kamata ku sani kan cutar limoniya

Ana wa yara ƙarin ruwa a kan matakala a wani asibitin yara da ke birnin Beijing a ranar 23 ga Nuwamba, 2023.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Nuwamban shekarar 2023, kafafen yaɗa labarai na ƙasar China waɗanda ba na gwamnati ba sun ba da rahoton cewa asibitocin kananan yara a sassan kasar sun cika dayara marasa lafiya.
An wallafa

An ba da rahoton samun ƙarin kamuwa da cutukan da ke shafar hanyar shaƙar iskar kamar Limoniya a duk duniya kwanan nan, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba.

A watan Nuwamban shekarar 2023, hukumar kula da lafiya ta kasar China ta ba da rahoton cewa, an samu karuwar cututtuka da dama a kasar, wadanda suka hada da mura da cutar korona da kuma limoniya - ƙwayar cututtuka da aka sani ke shafar ƙananan yara.

Sai dai daga baya, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta fayyace cewa, ba a gano wasu kwayoyin cutar da ke haifar da fargaba ba ga yara masu fama da ciwon limoniya a ƙasar China.

Wannan shi ne lokacin hunturu na farko tun bayan kulle a China sakamakon tsaurara takunkumin cutar korona.

Hukumar ta WHO ta danganta cutar limoniya da tazarar rashin bai wa yaran da aka ware lokacin korana kariya wanda hakan ka iya haifar da ɓarkewar annoba da zarar kamuwa da cutar ta dawo.

Sauran ƙasashe, ciki har da Birtaniya da Faransa da Denmark da kuma Amurka, su ma sun ga irin wannan cutar na limoniya tun lokacin da aka ɗage takunkumin kulle a lokacin korona.

A cewar WHO, cutar limoniya ita ce mafi girma da ke haifar da mutuwar yara a duniya.

Cutar ta kashe yara 740,180 'yan kasa da shekaru 5 a cikin shekarar 2019, wanda ya kai kashi 14 cikin 100 na duk mutuwar yara a wannan rukunin.

An fi samun mace-mace a kudancin Asiya da yankin kudu da hamadar Sahara.

Ga abubuwa biyar da ya kamata mu sani game da cutar limoniya.

likita na dubu yadda zuciyar jaririn ke bugawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana iya kamuwa da cutar limoniya ta jiyan, balantana lokacin haihuwa ko jim kaɗan bayan haihuwa.

Me nene cutar limoniya

A cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NFID), cutar limoniya ita ce kumburin huhu da ƙwayoyin cuta ke haifarwa.

Kowane mutum na iya samun limoniya, amma wasu mutane na cikin hatsari mafi girma.

Yara ƙanana da tsofaffi ko kuma mutanen da ke da wasu cututtuka masu tsanani kamar cututtukan zuciya da ciwon suga da cututtukan huhu da cututtukan da ke raunana tsarin rigakafi da wasu cututtukan daji, sun fi sauƙin kamuwa da limoniya.

Mece ce alamar kamuwa da limoniya?

Alamomin da ke nuna cewa mutum ya kamu da limoniya sun haɗa da zazzaɓi da jin sanyi da tari da numfashi sama-sama da jin kasala.

Amma alamu masu tsanani sun haɗa da ɗaukewar numfashi da sepsis (cutar da ake kamuwa ta ƙwayoyin cuta da ke iya kisa) da ma mutuwa.

Gane cutar da wuri da kuma magani yana da mahimmanci don hana aukuwar cututuka masu tsanani.

Ƙungiyar huhu ta Amurka ta shawarci mutane da su nemi taimakon likitoci da zarar sun ji wasu alamu kamar kasa numfashi da kyau, samun launin shuɗi a cikin leɓunansu da kan yatsa da ciwon ƙirji da zazzabi mai zafi, ko kuma tari mai majina mai tsanani.

Ta ya ya cutar limoniya ke yaɗuwa?

Ana iya samun yaɗuwar limoniya ta hanya daban-daban. Kwayoyin cutuka da ake samu a hanci ko makogwaron yaro suna iya cutar da huhu idan sun shaƙe su.

Haka nan suna iya yaduwa ta ɗigon-ɗigon iska daga tari da atishawa, ko taɓa abubuwa da tura ƙwayoyin cuta akansu.

Ana buƙatar ƙarin bincike a kan ƙwayoyin cuta daban-daban da ke haifar da limoniya da kuma hanyoyin da ake yaɗa su, saboda wannan yana da mahimmanci ga magani da rigakafi.

Lumoniya cuta ce da kuma kumburin huhu da ƙwayoyin cutuka daba-daban za su iya haifar wa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lumoniya cuta ce da kuma kumburin huhu da ƙwayoyin cutuka daba-daban za su iya haifar wa

Ta yaya za a iya magance cutar limoniya?

Ana ba da shawarar amfani da magungunan rigakafi idan za a iya magance cutar da su - wasu mutane ba za su buƙaci maganin rigakafi ba.

Yawancin mutane suna samun sauƙi a cikin makonni biyu zuwa hudu.

Duk da haka, wasu mutane sun fi fuskantar hatsarin kamuwa da rashin lafiya mai tsanani kuma suna iya buƙatar zuwa asibiti don magani.

A asibiti, yawanci ana ƙarawa mutane ruwa da maganin rigakafi, tare da iskar oxygen don taimaka musu numfashi.

Haka nan ana iya yi musu hoton duba lafiyar ƙirjinsu da gwajin jini don bincika wasu yanayi.

Ta ya ya zan kiyaye kamuwa da cutar limoniya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutane za su iya ɗaukar wasu matakai kuma su kiyaye kamuwa da limoniya.

Allurar rigakafi na iya kiyaye kamuwa da limoniyar da ƙwayar cututtuka suka haifar.

Amma cibiyar zuciya da huhu da kuma jini ta Amurka ta ce allurar rigakafin limoniya ba za ta iya kiyaye duka nau'in cutar ba.

Saboda haka idan aka kwatanta da mutanen da ba sa karɓar alurar rigakafin, waɗanda aka yi wa kuma duk da haka suna fama da limoniyar, ba su cikia samun cutar ta tsananta ba kuma limoniyar ba ta daɗewa a jikinsu

Wasu matakai ko hanyoyin da za su iya kiyaye mutum daga kamuwa da limoniya sun hada da tsafta mai kyau kamar wanke hannaye akai-akai, daina shan taba, kiyaye garkuwan jikinmu ta hanyar motsa jika na yau da kullum, da cin abinci mai kyau

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Burtaniya (NHS) ta ba da shawarar mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da limoniya mai tsanani su karɓi rigakafin cutar da ake kira da 'pneumococcal vaccine'

Wannan rigakafin kuma yana taimakawa wajen kariya daga wasu nau'ikan cututtuka na ƙwayoyin cuta waɗanda za su iya haifar da cutuka masu tsanani kamar cutar sankarau da cutuka a cikin kwakwalwa da kashin baya da kuma wani cuta da ake cewa 'sepsis' (wata cuta da za ta iya yin kisa).