Barcelona ta koma Europa League bayan shan kashi a hannun Bayern

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta kara doke Barcelona gida da waje a kakar nan a gasar Champions League wasa na biyar a rukuni na uku da suka kara ranar Laraba.
Minti 10 da fara wasa Sadio Mane ya ci Barcelona a Nou Camp, sannan Maxim Choupo-Moting ya kara na biyu.
Bayan da suka yi hutu ne suka koma zagaye na biyu, sai Benjamin Pavard ya kara na biyu daf da za a tashi daga wasan.
Ranar 13 ga watan Satumba, Bayern Munich ta doke Barcelona 2-0 a Jamus a karawar cikin rukuni.
Inter Milan ta casa Victoria Polzen 4-0 a ranar Laraba, hakan ya sa ta zama ta biyu a kan teburin rukuni na uku.
Bayern Munich ce ta daya mai maki 15, sai Inter Milan ta biyu mai maki 10, yayin da Barcelona keda maki hudu, ita kuwa Polzen ba ta da ko daya.
Da wannan sakamakon Bayern Munich ta ja ragamar teburin rukuni na uku ta kai zagaye na biyu tare da Inter Milan.
Ita kuwa Barcelona za ta koma buga Europa League karo na biyu a jere, bayan da ta kasa kokari da ta kai Eintranch Frankfurt ta yi waje da ita a bara.
Wannan shi ne wasa na 15 da suka fafata a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda kungiyar Jamus ta yi nasara a 11 da canjaras biyu, Barca ta ci biyu.
Ranar 2 ga watan Nuwamba za a buga wasan karshe a rukuni na uku tsakanin Bayern da Inter Milan da wanda Barcelona za ta ziyarci Polzen.
Yan wasan Barcelona da za su fuskanci Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Tuni kociyan Barcelona, Xavi Hernandez ya bayyana 'yan wasa 21 da zai suskanci Bayern Munich da su.
Ter Stegen, Bellerín, Piqué, Sergio, O. Dembélé, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Marcos A., Jordi Alba da kuma Kessie.
Sauran sun hada de De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Iñaki Peña, Balde, Gavi, Pablo Torre da kuma Arnau Tenas.









