Me ya faru da iyalan Bibas na Isra'ila da Hamas ta miƙa gawarwakinsu?

Asalin hoton, Reuters
Shiri Bibas da ƴaƴanta biyu - waɗanda ƙungiyar Hamas ta ce an kashe su a wani harin Isra'ila ta sama a farkon yaƙin - sun zama babban abin magana game da harin da Hamas ɗin ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda kuma ya jawo yaƙi a Gaza.
Lokacin da ƙungiyar ta bayar da gawarwarkin mutanen da ta yi garkuwa da su ranar Alhamis a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta, ta ce cikinsu akwai Shiri Bibas da kuma ƙananan 'ya'yanta biyu Ariel da Kfir.
Sai dai rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce gwaje-gwajen da ta yi sun nuna cewa ɗaya daga cikin gawarwakin ba na Shiri Bibas ba ne kuma ta zargi Hamas da karya ƙa'idojin yarjejeniyar.
An ce sauran biyun ƴaƴanta ne, Ariel da Kfir.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi zargin cewa "Hamas ta saka gawar wata mace Bafalasɗiniya a cikin makara".
Wani mai magana da yawun Hamas ya faɗa a dandalin X ranar Juma'a cewa akwai yiwuwar an gwamutsa gawar Shiri ne da wasu da ɓaraguzan gini suka danne bayan wani harin Isra'ila.
Ƙungiyar ta ce za ta bincika lamarin domin gano abin da ya faru.
Su wane ne iyalan Bibas?
Shiri na da shekara 32, yayin da Ariel ke da ke da shekara huɗu, Kfir kuma ke da wata tara da haihuwa.
Hoton uwar cikin firgici rungume da 'ya'yan nata lokacin da ake awon gaba da su zuwa Gaza na cikin waɗanda aka fi magana a kansu a wannan ranar.
An kama su ne tare da mahaifinsu Yarden daga rukunin gidaje na Nir Oz bayan ɗaruruwan mayaƙan Hamas sun tsallaka iyakar Gaza da kudancin Isra'ila.

Asalin hoton, PA
Kazalika, an kashe iyayen Shiri a harin na Hamas.
Kfir ne mafi ƙanƙantar shekaru cikin mutanen da aka sace zuwa Gaza su 251.
Me ya faru da su?
A watan Nuwamban 2023, Hamas ta ce an kashe Shiri da 'ya'yanta sakamakon wani harin da Isra'ila ta kai, amma ba ta bayar da wata hujja ba.
Jami'an Isra'ila ba su tabbatar da iƙirarin na Hamas ba amma sun ce sun damu sosai game da rayukan mutanen nasu da ake garkuwa da su.
Bayan an bayar da gawarwakin nasu a ranar Alhamis 20 ga watan Fabrairu, IDF ta ce "kisan gilla aka yi wa yaran lokacin da suke hannun Hamas" bisa gwaje-gwajen da suka yi da kuma bayanan da suka tattara.
A martaninta, Hamas ta jaddada abin da ta faɗa a baya, tana mai cewa hare-haren Isra'ila ne suka kashe yaran da uwarsu.
Yaushe aka sako Yarden Bibas?

Asalin hoton, Reuters
A farkon watan Janairun 2025, sunayen Shiri, da Yarden, da Ariel, da Kfir Bibas sun bayyana a cikin jerin mutum 34 da Hamas ta ce za ta iya sakowa a zangon farko na yarjejeniyar tsagaita wuta da ta ƙulla da Isra'ilar.
An fara aiki da yarjejeniyar ranar 19 ga watan Janairu, inda sai a 1 ga Fabrairu aka sako Yarden mai shekara 34 tare da wasu mutum biyu a madadin Falasɗinawa 183 da ke gidajen yarin Isra'ila.
Yaushe Hamas ta saki gawarwakin?
A farkon wannan makon, Hamas ta sanar cewa za ta saki gawarwakin Isra'ila, ciki har da Shiri da 'ya'yanta biyu.
A ranar 20 ga Fabrairu, Isra'ila ta tabbatar da sakin gawa huɗu ta hannun ƙungiyar agaji ta Red Cross a wani dandali da ke yankin Khan Younis.
Ƙungiyar ta ce gawarwakin na iyalan Bibas ne.
Ta huɗun kuma ta wani ɗan gwagwarmaya ce Oded Lifschitz mai shekara 84.
Cikin shewa da nuna iko kamar yadda aka saba gani yayin miƙa mutanen da take garkuwa da su, an ɗora makara huɗu baƙaƙe a kan wani dandamali a Khan Younis da ke kudancin Gaza a gaban dandazon 'yankallo.
An ga wani jami'in Red Cross na saka hannu kan wasu takardu a kan wani teburi a kusa dakarun Hamas masu ɗauke da makamai, kafin daga baya a fita da gawarwakin a cikin motar Red Cross.
An kai su cibiyar gwaji na Abu Kabir da ke Jaffa a birnin Tel Aviv na Isra'ila domin gudanar da gwaje-gwaje.

Asalin hoton, Reuters
'Yan awanni bayan haka, IDF ta wallafa saƙo a dandalin X cewa: "Sakamakon bincike, an gano cewa ɗaya daga cikin gawarwakin ba ta Shiri Bibas ba ce, kuma ba a samu dacewa a kan wani mutum daban cikin mutanen. Ba a iya gane wannan gawar ba."
"Wannan saɓa yarjejeniya ne matuƙa da Hamas ta aikata, wadda aka yi yarjejeniya da ita domin sakin gawa huɗu. Muna neman Hamas ta sako Shiri tare da dukkan mutanenmu."
Wani mai magana da yawun Hamas, Ismail al-Thwabta, ya faɗa a dandalin X cewa akwai yiwuwar an gwamutsa gawar Shiri ne da wasu waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai bayan harin Isra'ila.
Ƙungiyar ta faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa za ta bincika abin da ya faru game da gawar da aka tura Isra'ila.
An amince da sakin gawarwakin ne a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta, inda Isra'ila ta ce tana sa ran a sako mata gawar mutum takwas.











