West Ham za ta ɗauki Mohammed Kudus daga Ajax

Mohammed Kudus

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

West Ham United na tattaunawa da Ajax kan yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na kasar Ghana Mohammed Kudus da niyyar kawo shi London.

Dan wasan mai shekaru 23 ya zura kwallaye uku a wasan da Ajax ta doke Ludogorets a wasan share fage na neman shiga gasar cin kofin Europa a Bulgaria ranar Alhamis.

Wakilan West Ham sun ziyarci filin wasan, inda dan wasan na Ghana ya ce watakila ya kasance wasansa na ƙarshe da kungiyar ta Holland.

Kudus ya kasance abin sha'awa sosai daga kungiyoyin Premier a wannan bazarar.

An fahimci cewa Brighton ta cimma yarjejeniya da Ajax kan Kudus a farkon wannan watan, amma sun kasa samun daidaitawa da dan wasan.

Kudus ya fara taka leda a kungiyar Nordjaelland ta kasar Denmark a shekarar 2018, kafin ya koma Ajax a shekarar 2020, inda ya zura kwallaye 27 a wasanni 87, ya kuma taimaka wa kungiyarsa ta lashe kofunan gasar Eredivisie biyu.

Ya zura kwallaye 11 a wasanni 30 da ya buga na Eredivisie a kakar wasan da ta wuce yayin da Ajax ta zo ta uku.

West Ham ta kuma sayi dan wasan tsakiya James Ward-Prowse daga Southampton da kuma mai tsaron baya Konstantinos Mavropanos daga Stuttgart a farkon wannan watan.