Me zaman fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado ke nufi?

Asalin hoton, Kamfa
A ranar Litinin ɗin nan ne Sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani a Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi zaman fada a gidan Sarki da ke Nassarawa.
Wannan dai na zuwa ne sakamakon saɓata juyata da ake samu tsakanin ɓangarensa da na wanda gwamnatin jihar Kano ta ayyana a matsayin sabon Sarki, Muhammad Sanusi II, bayan rushe masarautun jihar guda biyar da majalisar dokoki ta yi.
Alhaji Aminu Ado Bayero dai ya koma Kano ne inda ya ce shi ne Sarkin na Kano sakamakon wata takarda da wata babbar kotun tarayya ta fitar tana umartar gwamnatin Kano da ta dakata da matakan da ta ɗauka.
To sai dai gwamnatin Kanon ta bakin Kwamashinanan Shari'a Haruna Isa Dederi, ta ce sai bayan sun aiwatar da duk abubuwan da kotun ta hana sannan suka ga umarnin nata.
Kotun dai ta saka 3 ga watan Yuni a matsayin ranar sauraron ƙarar.
Yanzu dai abin tambaya shi ne me wannan zaman fadar na Sarkin Kanon na 15 ke nufi?
Yadda zaman fadar ya kasance

Asalin hoton, Kamfa
Cikin kayan ƙasaita da suka haɗa da alkyabba da rawani mai kunne biyu kuma riƙe da tagwayen masu, Sarkin dai na 15 ya zauna a fadar ta Nasarawa a safiyar yau, inda fadawa da hakimai suka kai gaisuwa da caffa.
Sai dai kuma sabanin yadda aka saba, Alhaji Aminu Ado ya fita riƙe da tagwayen masu sannan kuma aka bude masa lema waɗansu al'adu da aka kebance wa sarki mai cikakken iko.
Bayanai sun nuna cewa fiye da hakimai fiye da 10 da wakilan wasu hakiman su ma fiye da 10 ne suka kasance tare da Alhaji Aminu Ado Bayero daga masarautun aka rushe guda biyu, wani abu da ke nuni da yadda da dama daga cikinsu suke nuna goyon bayansu ga sarkin na 15.
Daga nan ne kuma Sarkin na 15 ya hau doki inda zagage suka kasance tare da shi cikin busa kakaki da algaita da banga da kuma waza baya ga harba bindaga , waɗansu alamu da ke nuni da sarki mai cikakken iko.

Asalin hoton, Kamfa
Me zaman fadar ke nufi?

Asalin hoton, Kamfa
Ibrahim Hussaini Kaikomom Makama wanda masanin harkokin fadar Kano ne ya ce ce akwai alamomin tambaya kan wannan zama bisa wasu dalilai biyu:
- Tagwayen Masu: Shi ne sandan da Sarki ke riƙewa mai ɗauke da masu guda biyu a samansa. Kuma sandan guda biyu ɗaya na azurfa ɗaya kuma mai kan gwal. Shi na gwal shi ne ake fita da shi wurin taro, wanda yake hannun Sarki na 15, Aminu Ado. Shi kuma na azurfa shi ne wanda yanzu yake hannun Sarki Sanusi wanda shi ana amfani da shi wajen zuwa masallaci ko kuma taron addini. Sai kuma tagwayen masu na usuli shi ne wanda ke hannun Kilishin Kano wanda sarki ke ɗagawa a lokutan karɓar gaisuwa a ranar Idi.
- Rashin bayyanar masu naɗa Sarki: Masanin ya ce sakamakon rashin bayyanar mutum biyar masu naɗa sarki a zaman fadar na Alhaji Aminu Ado Bayero na nuni da cewa akwai wani abu. Hakiman kuwa su ne Sarkin Bai da Madaki da Sarkin Dawaki Mai Tuta da Makama.
- Tara ta Kano: Ibrahim Hussaini Kaikomon Makama ya ce rashin bayyanar wasu masu rawani da ake kira tara ta Kano a wajen zaman fadar na nuni da cewa akwia sauran runa a kaba. Mutum tara da ake kira tara ta Kano sun haɗa da Waziri da Galadima da Wambai da Ɗan Iya/Barde da Turaki da Ciroma da Sarkin bai da Makama da Madaki.













