Wa yake iko da sassan Syria?

    • Marubuci, Daga Tawagar Zane-Zane ta BBC
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Cikin mako biyu kacal, mayaƙan 'yantawaye suka mamaye manyan garuruwa tun daga maɓoyarsu a arewaci zuwa Damascus babban birnin ƙasar.

Sun yi nasarar kifar da gwamnatin Bashar al-Assad bayan shekara 13 ana gwabza yaƙin basasa.

Haye kan motoci da babura, mayaƙan ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) sun kutsa cikin sauri ta babbar hanya tsakanin kudu da arewa ba tare da fuskantar wata turjiya ba.

Makomar ƙasar na cikin taraddadi bayan kifar da gwamnatin iyalan Assad ɗin da suka shafe kusan shekara 50 suna mulkin ƙasar ta Gabas ta Tsakiya.

Sai dai kuma, yanzu haka ƙungiyoyin 'yantawaye daban-daban ne ke iko da sassan ƙasar, kuma mun duba wuraren da kowace ƙungiya ke iko da su.

Wa ke iko da yankunan ƙasar?

Faɗuwar gwamnatin Assad ta faru ne sakamakon yunƙurin mayaƙan tawayen na bazata ƙarƙashin ƙungiyar HTS.

Duk da cewa HTS ɗin ce ke iko da manyan birane, akwai wuraren da ba su hannunta a ƙasar.

Da ma sassan ƙasar sun shafe shekaru a hannun mayaƙan tawaye kamar HTS da ke iko da Idlib, da mayaƙan Kurdawa masu iko da garuruwan arewa maso gabas.

Babu ƙungiyar da ke jajanta abin da ya faru da gwamnatin Assad, amma kuma za a fuskanci matsaloli wajen haɗa kan ƙungiyoyin domin su mulki ƙasar tare.

A 'yan kwanakin nan ma an fafata tsakanin wasu ƙungiyoyin da ke adawa da juna a arewaci.

Ta yaya 'yantawayen suka kai birnin Damascus?

Bayan shafe shekaru suna laɓewa, mayaƙan sun yunƙuro tare da kifar da gwamnati a ƙarshen makon da ya gabata.

Bayan sun ƙwace iko da birnin Aleppo na biyu mafi girma a ƙasar a ƙarshen watan Nuwamba, sun ci gaba da kutsawa kudanci don ƙwace Hama ranar Alhamis da ta wuce.

Sun ci gaba babu ƙaƙƙautawa zuwa gari na uku wato Homs, kafin daga baya su kame birnin Damascus.

A ina Syria take kuma yaya maƙwabtanta suka ji?

Syria mai al'umma miliyan 22, na gabas da Tekun Baharrum ne. Tana maƙwabtaka da Turkiyya ta arewaci, Lebanon da Isra'ila ta yammaci da kudu maso yamma, da Iraƙi ta gabashi, sai kuma Jordan ta ɓangaren kudanci.

Turkiyya da wasu ƙasashen Larabawa da Turawa na mara wa mayaƙan tawaye daban-daban baya da ke adawa da gwamnati a yaƙin.

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, da ke samun goyon bayan Iran, ta taya sojojin gwamnati yaƙi, amma kuma ta samu matsaloli tun bayan fara yaƙinta da Isra'ila. Ana kallon hakan cikin dalilan da suka jawo faɗuwar gwamnatin ta Assad.

Wane martani Isra'ila ta mayar?

Jiragen yaƙin Isra'ila sun ƙaddamar da ɗaruruwan hare-hare a faɗin Syria, inda suka dinga lugude kan makamai da sansanonin sojin ƙasar, da filayen jirgin sama, da cibiyoyin bincike.

Ƙungiyar Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) da ke Birtaniya ta ce Isra'ila ta kai hare-haren sama da 300 tun bayan faɗuwar gwamnatin Assad ranar Lahadi.

Rahotonni na cewa akasarin wuraren da aka kai wa hari sun lalace baki ɗaya.

Isra'ilar ta ce ta yi hakan ne saboda kada makaman su faɗa hannun "masu tsattsauran ra'ayi".

Isra'ila ta kuma ce ta kame iko da wani yanki da ya raba iyakarta da Syria a cikin Tuddan Golan, tana mai cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Syria ta "daina aiki" bayan 'yantawayen sun ƙwace iko.

Ta musanta rahotonnin cewa tankunan yaƙinta sun nufi birnin Damascus, amma dai dakarunta sun shiga wasu yankuna na Syria.

Tuddan Golan yanki ne mai duwatsu da tsaunuka mai nisan kilomita 60 daga Damascus.

Isra'ila ta ƙwace shi a yaƙin 1967 na kwana da shida da ta gwabza da ƙasashen Larabawa, kuma ta ayyana iko da shi a 1981. Sai dai ƙasashen duniya ba su amince da matakin ba, duk da cewa Amurka ta yi hakan ita kaɗai a 2019.

Me ke faruwa a arewacin Syria?

A garin Manbij da ke arewacin ƙasar, mayaƙan da ke samun goyon bayan Turkiyya sun fafata da na Kurdawan da ke iko da wasu yankuna.

Kowace ƙungiya na iƙirarin ƙwace wani ɓangare na birnin, kuma rahotonni na cewa ana ci gaba da gwabzawa a wasu unguwanni.

Masu nazari a cibiyar Institute for the Study of War mai kula da rikici na cewa ba su da tabbas game da wanda ke iko da birnin na Manbij.

Sansanonin Rasha a Syria

A 2015, Rasha ta tura dubban dakaru zuwa Syria domin tallafa wa Shugaba Assad dawo da ƙarfin ikonsa.

A madadin haka, an bai wa Rashar lasisin zama a sansanoni biyu tsawon shekaru 49.

Gaɓar ruwa da ke Tartous, shi ne sansanin sojan ruwa na Rasha mafi girma a ƙasashen waje kuma ɗaya tilo a Tekun Baharrum.

Tare da sansanin sojin sama na Hmeimim, da ake yawan amfani da shi wajen kai dakaru ƙasashen Afirka, sansanonin na taka muhimmiyar rawa wajen nuna ƙarfin ikon Rasha a duniya.

Fadar Kremlin ta ce za ta tattauna da sabuwar gwamnatin Syria game da sansanonin nata.