Barcelona ta ragargaji Red Star a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta je ta caskara Red Star Belgrade da cin 5-2 a Champions League da suka kara ranar Laraba a Serbia.
Minti na 13 da fara wasa ne Barcelona ta fara cin ƙwallo ta hannun Inigo Martinez daga baya Red Star ta farke ta hannun Katompa Mvumpa.
Daga nan Barcelona ta kara biyu ta hannun Robert Lewandowski, sai kuma Raphinha da ya ci na huɗu a fafatawar.
Saura minti shida a tashi daga wasan Red Star ta kara zare ɗaya ta hannun Milson, kafin nan Barcelona zura na biyar a raga ta hannun Fermin Lopez.
Kawo yanzu Barcelona ta ci karawa uku da rashin nasara ɗaya daga wasa huɗun da ta yi a gasar ta zakarun Turai ta kakar nan.
Wannan shi ne karo na takwas da suka kece raini a tsakaninsu a babbar gasar zakarun Turai, inda Barcelona ta yi nasara huɗu da canjaras biyu aka doke ta biyu daga ciki.
Ƴan wasan da Hansi Flick ya bayyana su 22 da ya je da su Serbia, da suka doke Red Stars Belgrade.
Ƴan wasan Barcelona:
Cubarsí, Balde, I. Martinez, Gavi, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre, Fermín da kuma M. Casadó.
Sauran sun haɗa da Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Kounde, Szczesny, Astralaga, H. Fort, Gerard Martín da kuma S. Domínguez.
Wasan da Barcelona za ta fuskanta nan gaba
Barcelona wadda take ta ɗaya a kan teburin La Liga da tazarar maki tara tsakani da Real Madrid ta biyu, za ta je gidan Real Sociedad ranar Asabar a gasar ta La Liga.
Daga nan kuma Celta Vigo za ta karɓi bakuncin Barcelona a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024.











