'Sanyin' Ingila ba zai bar Mbappe tafiya Arsenal ba, Nice za ta hana Man Utd Todibo

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kylian Mbappe, ya ce ba ta yadda zai koma Arsenal a bazara, inda ya yi barkwanci da cewa, Ingila tana da sanyi sosai a lokacin. (Mail)

Arsenal ta kammala cinikin matashin dan wasan Wales, Brayden Clarke, mai shekara 16, daga Wolves. (Standard)

Chelsea za ta yi wa dan wasan gaba na gefe na Ingila Cole Palmer karin albashi mai yawa kasa da shekara daya da matashin dan wasan ya koma can daga Manchester City. (Star)

Manyan kusoshin Nice za su hana duk wani yunkuri na Manchester United na sayen dan bayan kungiyar, Jean-Clair Todibo, dan Faransa mai shekara 24. (Football Insider)

RB Leipzig ta bai wa Tottenham Hotspur wa'adi kan ta yunkuro ta sayi dan wasan gaba na Jamus Timo Werner, wanda tun a watan Janairu yake zaman aro a kungiyar ta London. (Express)

Manchester City na san fara tattaunawa da golanta, Ederson na Brazil a kan sabon kwantiragi. (Star)

Newcastle United da Chelsea za su fafata a kan zawarcin matashin dan wasan gaba na gefe na Lyon Rayan Cherki, dan Faransa mai shekara 20, a bazara. (Fichajes )

Dan bayan Bayern Munich, Kim Min-jae, dan Koriya ta Kudu, wanda a baya Manchester United ke sonshi, ba ya jin dadi a inda kungiyar ke sa shi wasa a yanzu. (t-online dagaFootball Transfers)

Da wuya Manchester United ta sayi Sofyan Amrabat da ke zaman aro a wajen yanzu, daga Fiorentina a bazaran nan to amma Juventus na saha'awar dan wasan na Moroko. (Gazzetta dello Sport )

Dan wasan gaba Ivan Toney, dan Ingila ya yi barkwanci da cewa idan har ya bar Brentford a bazaran nan to ba inda zai tafi sai Madrid. (Sky Sports)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barcelona za ta sake komawa zawarcin dan wasan tsakiya na Feyenoord, Mats Wieffer na Netherlands. (Sport )

Dan wasan gaba na Barca, Raphinha, na Brazil na daya daga cikin 'yanwasan da kungiyoyin gasar saudiyya ke burin dauka a bazaran nan. (Sport)

Tuni kuma kungiyar Al-Ahli ta Saudiyyar ta bayyana sha'awarta a kan sayen dan wasan tsakiya na Argentina Rodrigo de Paul, na Atletico Madrid. (Fichajes )

Kociyan Ingila Gareth Southgate ya gaya wa Mason Greenwood na Manchester United cewa ba ya cikin tsarinsa a gasar cin kofin kasashen Turai ta wannan shekara (Euro 2024), amma kuma bai kawar da yuwuwar kiran dan gaban mai shekara 22 ba wanda ke zaman aro ayznu a Getafe, a karshen wasannin bazaran nan ba. (Express)

Tsohon dan gaba Manchester United Ruud van Nistelrooy ya yi watsi da tayin aikin kociya a Turai, saboda a Ingila yake son ya yi aiki. (Mirror)

Masu kungiyar Liverpool, wato Fenway Sports Group na duba yuwuwar sayen wata kungiyar gasar Amurka ta MLS. (Football Insider)

Watakila a tilasta wa Arsenal ta hana duk wani yunkuri na kociyan Faransa Thierry Henry na zabar William Saliba domin buga wa Faransa gasar Olympics ta Paris, a bazaran nan saboda hakan zai iya hana dan bayan mai shekara 22, damar halartar wasannin farko-farko na kakar 2024-25. (Mirror)