Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan dimbin bashin da ke kan kasar
Sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar a wannan makon cewa za ta karbo karin bashin naira tiriliyan 11 domin tafiyar da kasafin kudin 2023 ta janyo muhawara a kasar.
Dokar harkokin karbar bashi ta nuna cewa karin bashin da Najeriya za ta karbo ya zarta adadin kudin da aka amince ta ranto.
Ministar harkokin Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed wadda ta sanar da karbo bashin, ta ce za a karbo bashin ne daga cikin gida da kuma kasashen duniya.
Bayanai daga ofishin da ke da ke kula da bashi da lamuni na Najeriya sun nuna cewa ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022 jimillar bashin da ake bin kasar ya kai $100bn, kwatankwacin naira tiriliyan 42.
Kididdiga ta nuna cewa bashin da kasar ta karbo daga kasashen waje ya kai dala biliyan $40, kwatankwacin naira tiriliyan 17.
Kazalika ta karbi bashin biliyan $60, kwatankwacin naira tiriliyan 25 a cikin gida - wanda ya kunshi gwamnatin tarayya da gwanatocin jihohi da babban birnin tarayya.
Batun dai ya raba kawunan 'yan Najeriya, inda wasu ke cewa babu laifi idan kasar ta karbo bashin muddin za ta yi amfani da shi wajen harkokin gina kasa.
Sai dai wasu na ganin karbo bashin a matsayin kara jefa kasar cikin kangin bashi da tsadar rayuwa, suna masu cewa duk da basukan da ta karbo a baya 'yan kasar na kara fadawa cikin mawuyacin hali.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Ƴan Najeriya musamman masu bibiyar shafin Twitter da Facebook na BBC Hausa sun rika tsokaci da tafka mahawara game da batun yawan bashin da ake bin ta.
Wani mai binmu a shafin Facebook, Abu Abdurrahman, ya ce: "Lallai talaka zai sha matsa irin ta mai a jikin gyada. Allah ya sa mu wanye lafiya, domin wannan bashin duk a jikin talaka za a matso kudaden su fito ta hanyar tsadar kayan masarufi da kayan ayyukan yau da kullum."
Wani mai bin shafinmu na Twitter, Murtala Gaya ya ce: "Bashi hanji ne. Wanda ake bin Amurka ya ninka na Najeriya. Don haka ko yanzu ta kama a karo bashi Baba [Buhari]."
Ita ma Husna Abdul cewa ta yi: "Ba gwamnatin da ba ta cin bashi, kuma al'umma ake yi wa ayyukan raya kasa."
Amma Ayshatt Abubakar cewa ta yi: "Allah ya kyauta, bashi kam ya kai bashi da ma bashi yana hana abu ya ci gaba, ga mu nan sai jin jiki muke."
Murtala MG ya ce: "Babu matsala, ai bashi hanji ne yana cikin kowa. Da sannu za mu biya; kawai abin tambaya shi ne yaya aka kashe kudin?"
A nasa bangaren, Abdukadir Magaji Narimi, ya ce: "Wannan babban abin takaici ne - mafi takaici ma shi ne daga cikin bashin talaka bai amfana da komai ba."
Ali Adamu ya ce duk da bashin da kasar take ciyowa "babu wutar lantarki, babu hanyoyi masu kyau, babu ingantaccen kiwon lafiya, kungiyar malaman jami'a tana yajin aiki...a ina ake kashe kudin da ake karbowa bashi?"