Man Utd na shirin dawo da Gomes, Arsenal za ta tsawaita zaman Trossard

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na fatan sake ɗauko ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 24, Angel Gomes, a kyauta idan kwangilar sa da Lille ta ƙare. (Mail)

Haka nan kuma, United ta shirya fafatawa da Real Madrid a ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan gefen Atalanta, Ademola Lookman. Ƙungiyoyi da dama na shirin shiga zawarcin ɗan asalin Najeriyar mai shekara 27 a ƙarshen kakar wasan bana. (Caught Offside)

West Ham da Newcastle na daga cikin ƙungiyoyin gasar Firimiya da ke zawarcin ɗan wasan gaban Faransa, Kolo Muani, wanda PSG ke shirin bayar da shi aro. (Caught Offside)

Da alama Newcastle za ta jinkirta zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan bayan Ingila da Crystal Palace mai shekara 24, Marc Guehi, saboda murmurewar da 2 Sven Botman ya yi daga jinya. (Times - subscription required)

Arsenal na tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Belgium mai shekara 29, Leandro Trossard, a game da tsawaita kwangilarsa da ƙungiyar da kuma ƙarin albashi. (Mail)

Real Madrid na ci gaba da fatan ɗaukar ɗan wasan bayan Canada mai shekara 24, Alphonso Davies, daga Bayern Munich duk da raɗe-raɗin cewa ɗan wasan zai tsawaita kwangilar sa da ƙungiyar Jamus ɗin.(AS - in Spanish)

Tsohon shugaban Liverpool, Peter Moore ya ce masu ƙungiyar na shirin sabinta kwangilar ƴan wasansu da suka haɗa da ɗan wasan Masar mai shekara 32, Mohammed Salah da ɗan wasan bayan Ingila mai shekara 26, Trent Alexander-Arnold da kuma ɗan wasan Netherland mai shekara 33, Virgil Van Dijk. (Sky Sports)

Manchester City za ta ƙara jira har zuwa ƙarshen watan Maris kafin ta san makomar ta a game da hukuncin kwamitin ladabtarwa kan zargin karya dokokin kashe kuɗi da ake yi wa ƙungiyar ta gasar Firimiya. (Football Insider)

Kila Juventus ta ɗauke ɗan wasan bayan Chelsea mai shekara 27, kyauta a watan Janairu bayan ɗan wasan ya kasa samun shiga zaɓin farko a ƙungiyarsa. (Mail, external)