Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan wasan Leicester Fatawu zai yi jinya zuwa ƙarshen kaka
Kocin Leicester City Steve Cooper ya sanar da cewa ɗan wasan kungiyar na gefe Abdul Fatawu zai yi jinya zuwa ƙarshen kakar wasanni ta bana saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.
Dan wasan mai shekara 20 ya ji raunin ne a lokacin da yake yi wa Ghana wasa, a wasan da suka yi da Angola yayin da ake wasannin ƙasashe.
"Babu dadi abun, mummunan rauni ya ji," in ji kocin Leicester City wanda wanda zai karɓi baƙuncin Chelsea a Premier a ranar Asabar.
"Ya ji rauni a gwiwarsa da ba zai bar shi ci gaba da buga wasanni ba har zuwa ƙarshen kakar nan.
"Babban koma baya ne, na farko, matashi ne irin wannan raunin koma baya ne a wajensa.
"Yakan iya zama raunin da aka saba gani tsakanin 'yan kwallo, amma dai mummuna ne,".
Fatawu ya taimaka wa Foxes wajen dawowa Premier kuma ya zuwa yanzu ya buga mata wasa 11 a wannan kakar.
Shi ya ƙarfafawa Leicester gwiwa a nasarar da ta samu kan Southampton a ranar 21 ga watan Oktoba - lokacin da suka farke 2-0 da aka ci su suka ta shi 2-3.