Rashin buga gasar cin kofin duniya ya tsuma Haaland

An wallafa

Erling Haaland na amfani da damuwar da ya shiga na rashin buga gasar cin kofin duniya wajen zura ƙwallaye a gasar Firemiya ta Ingila.

Haaland ya ci ƙwallo 20 a cikin wasa 14 tun da ya koma Manchester City daga Dortmund.

Ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi kowane ɗan ƙwallo wajen zura yawan ƙwallaye 20 a ƙanƙanin lokaci.

A baya ɗan ƙwallon Sunderland Kevin Phillips ne ke da tarihin a lokacin yana Sunderland a shekara ta 2000.

"Ina zaune a gida, cikin fushi bana buga gasar cin kofin duniya," Haaland ya shaida wa Amazon Prime.

"Kallon wasu na cin ƙwallo a gasar cin kofin duniya ya tsuma ni. Ina ƙishirwan cin ƙwallo."

Guardiola ya ji daɗi sosai da ɗan ƙwallon wanda ya ɗauko daga Borussia Dortmund a kan fiye da fan miliyan 50 ya zura ƙwallo biyu a ragar Leeds.

Amma a cewar sa kamata ya yi Haaland ya ci ƙwallo biyar ba domin ƙwazon da golan Leeds Illan Meslier ya nuna ba.