Hojlund ya sa Man United ta raba maki a gidan Bournemouth a Premier

Rasmus Hojlund

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Rasmus Hojlund ne ya farke ƙwallon da Bournemouth ta ci Manchester United a Premier League da suka tashi 1-1 ranar Lahadi a Vitality.

Wannan sakamakon ya zama kalubale ga Bournemouth, wadda ke fatan shiga gurbin zakarun Tuari a baɗi.

Ƙungiyar da Andoni Iraola ke jan ragama ta fara cin ƙwallo ta hannun Antoine Semenyo tun kan hutu, kuma na 11 da ya zura a raga a bana kenan.

Sai dai an ci karo da takaddama a wasan a hukuncin da Evanilson ya yi wa Noussair Mazraoui keta a minti na 70, daga farko a bayar da katin gargadi, sai aka maye gurbinsa da jan kati, bayan da VAR ta fayyace hakan.

Da wannan sakamakon ƙungiyar da Ruben Amorim ke jan ragama ta koma ta 14 a teburi, wadda ke fatan lashe Europa League na kakar nan.

Ranar Alhamis United za ta je gidan Athletic Bilbao a wasan farko a daf da karshe a gasar ta Europa League.

Wannan sakamakon wasan ranar Lahadin ya zama koma baya ga Bournemouth, wadda Fulham da Brighton ke gabanta.

Bournemouth, wadda take ta 10 teburi na fatan samu gurbin shiga Conference League wato ta takwas, idan Crystal Palace ba ta lashe FA Cup ba.