Ƴan Real da suka je Bayern buga Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta ziyarci Bayern Munich, domin buga wasan daf da karshe a Champions League ranar Talata.
Wannan shi ne karo na 27 da za su kece raini a tsakaninsu a gasar ta zakarun Turai, inda Real ta yi nasara 12, Bayern ta ci karawa 11 da canjaras a tsakaninsu.
Wannan shi ne wasan farko da za su fuskanci juna bayan 2018 a gasar ta zakarun Turai, inda Real ta je ta ci 2-1 a Jamus, sai suka tashi 2-2 a Sifaniya.
Real Madrid tana da Champions League 14, wadda ta kawo wannan matakin bayan fitar da Manchester City.
Ita kuwa Bayern Munich mai kofin zakarun Turai shida ta kawo zagayen daf da karshe a bana, bayan yin waje da Arsenal.
Koda yake an yi waje da kungiyoyin Premier League a Champions League na bana, amma za a kece raini tsakanin 'yan kwallon tawagar Ingila biyu.
Kyaftin Harry Kane yana buga wa Bayern Munich wasa a kakar farko da cin kwallo 35 a bana daga Tottenham.
Shi kuwa Bellingham dake wasa a Real Madrid shima a kakar farko ya zura 17 a raga a La Liga da aka dauka daga Borussia Dotrmund.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Kepa.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger, Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos, Arda Güler.
Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu, Brahim.











