Newcastle ta nemi Ashworth ya fara hutu, Liverpool na zawarcin Alonso

Dan Ashworth

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan Ashworth
An wallafa

An ba darakan wasanni na Newcastle Dan Ashworth damar zuwa hutu bayan ya nemi barin kungiyar yayin da Manchester United ke zawarcinsa. (Athletic - subscription required)

Ya zama dole ga Manchester United din ta biya kungiyar diyya idan ta na son ta dauki Ashworth aiki ko kuma ta jira sai ya cika shekara biyu na hutun da aka rubuta a ciki kwantaraginsa da Newcastle . (Mail)

Chelsea na bibiyar halin da Harry Kane ya ke ciki a Bayern Munich yayin da rahotani ke cewa hankalin dan wasa mai hari na Ingila mai shekara 31 bai kwanta sosai a Jamus ba. (Football Insider)

Kylian Mbappe ya tattauna da Manchester City kwana guda kafin dan wasan Faransa mai shekara 25 ya sanar cewa zai bar Paris St-Germain a karshen kakar wasanni . (Cadena Ser - in Spanish)

Liverpool na fatan daukar kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso da darektan wasanni na kungiyar Simon Rolfes don maye gurbin Jurgen Klopp da Jorg Schmadtke wadanda za su bar kungiyar a bazara . (Football Insider)

Tottenham na zawarcin dan wasan tsakiyar Everton da Ingila James Garner dan shekara 22 . (Teamtalk)

Oliver Glasner ya amince ya maye gurbin kocin Crystal Palace Roy Hodgson karkashin yajejeniyar shekara biyu da rabi . (Sky Sports)

Arsenal ta na sha’awar dan wasan tsakiyar Red Bull Salzburg Oscar Gloukh kuma ta fara tunanin yi wa dan wasan Israila mai shekara 19 magana . (Football Transfers)

Tsohon kocin Wales Chris Coleman ya bayyana a matsayin wanda za a nada a matsayin kocin Jamhuriyar Ireland bayan da aka samu tsaiko a tattaunawar da ake yi da kocin tawagar kwallon kafar Ingila masu shekaru kasa da 21 Lee Carsley . (The Independent)

Ba za a kori kocin Bayern Munich Thomas Tuchel ba duk da cewa kungiyar ta Bundesliga ta sha kaye sau uku a jere a cikin kwanaki 9 a karawar da ta yi da Bochum ranar Lahadi.(Sky Germany)

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya nemi karin bayani a kan Roberto de Zerbi yayin da ya ke tunanin daukar kocin Brighton a matsayin wanda zai maye gurbin Xavi a karshen kakar wasanni (Sport - in Spanish)

Dan wasa mai tsaron bayan Birmingham da Jamhuriyar Ireland Kevin Long mai shekara 33 ya kusan kamala komawa kungiyar Toronto FC (Birmingham Mail)