Za a fara yi wa jarirai allurar rigakafin korona a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Masu lura da yadda ake bayar da magani a Amurka sun bayar da umurnin cewa yanzu za a iya yi wa jarirai 'yan wata shida rigakafin cutar korona.
Biden ya ce iyaye za su iya fara kai yaransu domin rigakafin a cikin makonni masu zuwa.
Amurka ce kasa ta farko a duk fadin duniya da ta amince a yi wa jarira 'yan wata shidda rigakafin na korona.
Wannan matakin zai sanya a samar da kananan kwalaben rigakafin ga yara kimanin miliyan 20.
A baya ba a yi wa yara rigakafin har sai sun kai shekara 5 ko fiye da haka.
Shugaban Biden ya bayyana lamarin a matsayin wani muhimmin mataki, wanda zai kara wa iyaye kwanciyar hankali.
Daraktar hukumar kare yaduwar cutuka ta Amurka Rochelle Walensky ta ce iyaye da dama sun zaku a yi wa yaransu rigakafin cutar.
To amma yanzu abin da ya rage a jira shi ne yawan mutanen da za su bukaci a bai wa yaran nasu allurar.
A bara ne aka amince a yi amfani da rigakafin na kamfanin Pfizer a kan yara daga shekara 5 zuwa 11.
Sai dai har yanzu kasa da kashi 30 cikin dari ne kawai na yawan yaran da suka kamata a yi wa rigakafin suka yarda aka yi masu cikakken rigakafin.











