Barcelona vs Eintracht Frankfurt: 'Yan Barca da za su kara da Frankfurt a Camp Nou

Asalin hoton, Barcelona FC
Eintracht Frankfurt ta ziyarci Barcelona, domin buga wasa na biyu a daf da na kusa da na karshe a Europa League da za su fafata a Camp Nou.
Kungiyoyin biyu sun tashi 1-1 a wasan farko da suka kece raini a Jamus ranar 7 ga watan Afirilu.
Frankfurt ce ta fara cin kwallo ta hannun Ansgar Knauff daga baya Barcelona ta farke ta hannun Ferran Torres.
Barcelona za ta buga wasan da kwarin gwiwa, bayan da Memphis da Sergino Dest suka koma taka leda, bayan da suka yi jinya ta makonni.
Tuni kociyan Barcelona Xavi ya bayyana 'yan kwallon da zai fuskanci Frankfurt.
'Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen, Dest, Pique, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Memphis, Adama, Braithwaite, Neto, Lenglet, Pedri, L. De jong, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Nico, Gavi, Balde da kuma Arnau Tenas.
Gerard Pique yana cikin 'yan wasan da aka bayyana, duk da ba a fayyace koshin lafiyarsa ba.
Ansu Fati, Sergi Roberto da kuma Samuel Umtiti na jinya, yayin da Dani Alves ba a yi masa rijistar buga gasar ba.











