Torres da Memphis Depay sun samar wa Barcelona maki uku

An wallafa

Barcelona ta sha da kyar a hannun Elche da ci biyu da daya bayan wani kyakkyawan sauyi da kocin kungiyar ya yi.

Gabanin tafiya hutun rabin lokaci Chaves de la Torre ya jefa kwallo daya bai ban haushi a ragar Barcelona a minti na 44.

Ana dawowa hutun rabin lokaci ne kocin Barcelona Xavi ya sako dan wasansa Ferran Torres ya farke wa kungiyar cikin wani salo mai kayatarwa.

Mai tsaron ragar Elche, Edgar Badia ya hana Torres kara kwallaye bayan tare masa wasu damarmaki masu yawa da ya yi.

Kazalika, Memphis Depay da aka sako a canji ya samu damar zira kwallo ta biyu ga Barcelona a bugun fenareti da ta samu abin da ya mayar da Barcelona matsayi na uku a teburin La Liga.

Kungiyar ta Catalan ta ci wasa shida cikin takwas da ta buga a baya, yayin dan wasan da ta dauko a watan Janairu Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallo a duka wasanni hudun da ya buga mata.

Yanzu dai Barcelona na matsayi na uku a gasar La Liga, inda take biye wa Sevilla da ke matsayi na biyu da maki 55 ita kuma Real Madrid da ke matsayi na daya da maki 63.

Barcelona dai na da wasa daya kwantai kuma ko ta ci wasan za ta ci gaba da kasancewa a bayan Sevilla.

Kungiyar da ke buga Europa za ta buga wasanta na gaba ne da Galatasaray, biyo bayan kora Napoli gida da ta yi.