Nijar: Mahara sun kashe farar hula 18 a Jamhuriyar Nijar

ISWAP

Asalin hoton, iSWAP

An wallafa

Mahukunta a jamhuriyyar Nijar sun ce an kashe fararen hula 18 a wani harin da 'yan bindiga suka kai a yammacin kasar.

Bayanai na cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai a kan babura ne suka kai hari kan wata babbar mota da ke jigilar mutane a tsakanin wasu kauyuka biyu da ke yankin Tillaberi.

Yammacin Nijar, kamar makwabtanta Mali da Burkina Faso sun shafe shekaru suna fuskantar hare-haren 'yan bindiga, duk kuwa da kokarin da dakarun kasa da kasa ke yi a yankin Sahel mai fama da kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

A halin da ake ciki dai kasashen biyu da ke makwabtaka da jamhuriyya Nijar na karkashin mulkin soji, bayan hambarar da gwamnatin farar hula.