Champions League: Karin batta tsakanin Madrid da PSG, Manchester City da Sporting Lisbon

PSG Madrid
An wallafa

Babu wai, a lokacin da PSG ta sayi Lionel Messi ba don ya taimaka mata bane ta lashe kofin gasar Ligue 1, sai don ya taimaka mata ta lashe kofin gasar zakarun turai.

Dama PSG ba ta taba lashe kofin zakarun turai ba duk da makudan kudin da masu kungiyar suka kashe wurin gina ta.

A 2020 sun buga wasan karshe da Bayern Munich amma dai suka yi rashin nasara 1-0.

A yanzu PSG na da yan gaba da duniya ta shedi cewa za su iya sauya kowace kungiya, wato Messsi da Neymar da kuma Mbappe.

Hakama PSG ta yi watsi da tayin fam miliyan 137 da Real Madrid ta yi kan Kylian Mbappe duk da cewa a watan Yuli kwantiraginsa ke karewa.

Saboda haka ba karamin buri kungiyar ta saka wa kofin gasar zakarun turan ba a bana.

A daya waje Real Madrid wadda za ta je bakunta Paris na da yan wasa da suka taka rawar gani sosai a matakin rukuni, kuma tana da mai horarwa da ke da kwarewa sosai a gasar.

Za a iya cewa samun koci a yanzu da ya fahimci gasar Champions League kamar Carlo Ancelotti a yanzu abu ne mai matukar wahala.

Kuma duk da Madrid ba ta kan ganiyarta kamar a da, za su iya gasa wa PSG aya a hannu a karawar.

Bugu da kari Madrid na da Karim Benzema da Eden Hazard a gaba, wadanda ba baki bane a wannan gasa.

Sai dai rauni zai hana a shedi haduwar tsohon mai tsaron bayan Madrid din Sergio Ramos da tsohuwar kungiyarsa wanda ya baro ta a bara zuwa PSG.

PSG Madrid

Asalin hoton, Getty Images

A daya wasan na yau da daddare Sporting Lisbon ce ke shirin karbar bakuncin Manchester City a Lisbon.

Manchester City ta lashe ko wane irin kofi da ake bugun gaba da shi a Ingila, to amma kofin gasar zakarun turai ne har yanzu ke ci gaba da yi mata kanshin dan goma.

Kungiyar ta kai wasan karshe bara, to amma da kyar Chelsea ta doke ta 1-0.

Saboda haka duk wani buri da Pep Guardiola da yan wasan suke da shi a bana na lashe kofin a bana, sai sun fara kawar da Sporting Lisbon a zagayen kungiyoyi 16.

Tuni tawagar City tana Lisbon, to amma ba tare da dan wasanta mafi tsada ba wato Jack Grealish da ta sawo daga Aston Villa fam miliyan 100.

Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Grealish zai bi sahun Cole Palmer da Gabriel Jesus da ke jinya saboda samun rauni.

To amma Guardiola na da kwarin gwuiwa cewa sun tafi da tawagar da za ta fitar da su kunya a Lisbon.

A karshen mako City ta ragargaza Norwich 4-0, a wasan da Raheem Sterling ya ci uku shi kadai.

A bangaren Sporting Lisbon masu sharhi na ganin duk da karfin kungiyar bai zo daya da na City ba, kungiyar wadda ta lashe kofin gasar Primeira Liga a karon farko bayan shekaru 19 na iya bai wa City mamaki.

Lisbon

Asalin hoton, Getty Images

Baya ga cewa tana gida, ana ta'allaka nasarorin da Sporting Lisbon ke samu a kan mai horar da kungiyar Ruben Amorim, wanda tsohon dan wasan Focugal ne.

A lokacin da kulob din ya biya yuro miliyan 10 kan Amorim daga kungiyar Braga B a 2020, tsohon dan wasan Focugal Luis Figo ya kwatanta hakan a matsayin hauka.

To amma daga zuwa ya ci wa kungiyar kofin Primeira Liga ya kuma kawo su wannan mataki a gasar Zakarun turai, hakan na nufin akwai bukatar Man City ta kalle shi a matsayin barazana.