Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PDP: Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya na shirin gudanar da babban taronta
Shirin babban taron jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ya kankama a Abuja babban birnin ƙasar, inda ake sa ran ƴaƴan jam'iyyar daga ko ina a faɗin Najeriya za su zaɓi manyan shugabanninta.
Wannan taron na zuwa ne bayan da wasu 'ya'yan jam'iyar suka shigar da kara a kotu domin a dakatar da gudanar da taron, sai dai ana jajibirin gudanar da shi kotu ta yi fatali da buƙatarsu, ta ce a ci gaba da shirin yin taron.
Sakataren jam'iyyar na ƙasa Sanata Umaru Ibrahim Tsauri, ya shaida wa BBC Hausa cewa an kammala dukkan wani shiri abin da kawai ake jira shi ne fara tantance waɗanda za su yi zaɓen, kana su ƙada ƙuri'a idan an jima.
A cewarsa ''Muna yi wa Allah godiya, domin matsayin da muke a yanzu ba a kan shi muke ba yanzu, jiya kamar yanzu muna tunanin shin za a yi taron ko ba za a yi ba don ana maganar kotu za ta iya dakatarwa, amma ga shi cikin ikon Allah kotu ta ce za a iya ci gaba da yi.''
Sakataren jam'iyyar ta PDP na Najeriya ya ƙara da cewa dama babban kalubalen da suke fuskanta a kan taron shi ne yiwuwar hanawa, ''domin shari'ar kamar mace ce mai ciki, amma mu ba mu yarda mu yi ƙasa a guiwa ba, sai da muka ga ko me za ta haifa mun kammala shirin suna, to Alhamdulillahi abin da muke bukata mun samu, kuma an kammala komi za a yi wannan taron.''
Shugabannin jam'iyyar mutum 21 za a zaɓa, da suka hada da yan kwamitin gudanarwar jam'iyyar su mutum 13, da mataimakansu guda 8, kuma su ne za su jagoranci jam'iyyar ta PDP daga ranar 8 ga watan Disamba har zuwa zaɓen 2023.
''Dukkan wani mataki da ake iya bi na ganin taron nan ya yi nasara to tsakani da Allah an bi shi, kuma an kawo matsaya abin da kawai muke jira shi ne anjima a tantance masu jefa ƙuri'a, a kaɗa kuri'a a kuma zaɓi shugabannin da za su jagorance mu zuwa samun nasara a zaɓukan 2023 idan Allah ya kaimu'' inji Sanata Tsauri.
Ya ce an dauki dukkan wasu matakai kama daga kan na tsaro da abinci da wurin zama da komai don gudanar da zaben.