Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin PDP: Kotu ta bai wa jam'iyyar damar gudanar da taron ƙasa
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Jihar Rivers ta yi watsi da ƙarar da tsohon shugaban PDP, Uche Secondus, ya shigar yana neman ta dakatar da babban taron jam'iyyar na ƙasa.
Cikin ƙarar da ya shigar, Mista Secondus ya nemi kotun ta hana babbar jam'iyyar adawar a Najeriya gudanar da babban taron da ta shirya yi ranar 30 da 31 ga watan Oktoba.
Daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotun, Secondus ya nemi ta ba shi wuƙa da nama na aiwatar da taron.
Tun farko tsohon shugaban ya sauka daga muƙaminsa biyo bayan rikicin da afku tsakaninsa wasu jiga-jigan jam'iyyar, musamman Gwamnan Rivers Nyesom Wike.
Rahotanni na cewa dukkan alƙalan kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani sun amince da hukuncin ba tare da jayayya ba.
Hukuncin na nufin PDP za ta ci gaba da shirin gudanar da taron, wanda a lokacin ne za ta zaɓi sabbin shugabanninta na ƙasa a muƙamai daban-daban.
Shirin taro ya yi nisa
Yayin wata ziyara da sashen Hausa na BBC ya kai babban filin taro na Eagle Square da ke Abuja, mun tarar da wuri ya ɗauki harami ana ta shirye-shiryen gudanar da zaben duk da rashin tabbacin gudanar da shi.
An sanya tutocin jam'iyyar a dukkanin faɗin filin, baya ga ƙyallaye masu launin fari da ja da kore, ga kuma babban mumbari da aka dirke a tsakiyar filin taron, inda a nan ne za a riƙa kaɗa ƙuri'a da kuma yin jawabi
Mambobin jam'iyyar daga ko'ina a fadin Najeriya sun taru a filin tun kafin wannan taro na ranar Asabar, inda suke aikin shirya kujeru da sauran kayayyakin da ake bukata don gudanar da taron.
Shugaban matasa na jam'iyyar, Honarabul SKE Odi Okoye wanda muka tarar a wajen taron da ya je a matsayin sakataren kwamitin shirya bababban taron, ya ce ba sa wata fargaba domina a cewarsa jam'iyyarsu na kan doka.
''Za mu ci gaba da ayyukanmu, sai dai in kotu ta yanke hukuncin hanawa, idan hakan ce ta tabbata, to jam'iyya za ta yi ganawar gaggawa domin sanin matakin da za ta ɗauka," a cewar Mista Okoye.
Wasu ƴaƴan jam'iyyar da suka hallara a filin sun ce suna da ƙwarin guiwar cewa taron zai gudana kamar yadda aka tsara, don haka suna nan daram-dam za su kafa su tsare don ganin wannan zaɓe ya gudana.
To shin idan kotu ta ce a fasa zaɓen fa?, tambayar kenan da muka yi wa Aishatu Muhammad Gwani wata ƴar jam'iyyar PDP daga jihar Bauchi, sai ta ce ''Haka za mu haƙura, ai mun saba ganin irin wannan, ba komi a ciki, a kan sa ranar zaɓe ma a daga ai'' inji ta.
Shi dai Uche Secondus na neman kotu ta dakatar da babban taron na ƙasa da babbar jam'iyyar adawar ta tsara gudanarwa ranar Asabar, lamarin da ka iya kawo cikas ga shirye-shiryen da PDP ke yi.