Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lewandowski zai koma City, Lingard zai bar United a Janairu
Mai kula da harkokin Robert Lewandowski, Pini Zahavi ya ce dan kwallon Bayern Munich zai iya komawa Manchester City a badi. (Bild - in German)
Watakila Raheem ya koma taka leda a Real Madrid ko Newcastle United ko Arsenal bayan da y ace zai iya barin Manchester City. (Express)
Leeds United na bibiyar dan kwallon Ajax mai shekara Noussair Mazraoui, wanda ake alakanta shi da zai koma Arsenal ko kuma Roma. (Football Insider)
Shugaban Lille, Olivier Letang ya ce a shirye suka su sayar da Renato Sanches ga duk kungiyar da ta yi tayi mai tsoka a Janairun nan. (Express)
An bayyana Cesar Azpilicueta tare da Andreas Christensen a matsayin wadanda Barcelona ke bibiyar wasanninsu, wadanda kwantiraginsu zai kara a kakar badi. (Fichajes - in Spanish)
Ana alakanta West Ham da Tottenham da cewar suna rububin son daukar mai tsaron ragar Saint-Etienne, Etienne Green. (TeamTalk)
Newcastle United ta tuntubi wakilan dan wasan Real Betis, Nabil Fekir, 28. (Footmercato - in French)
Jesse Lingard na shirin barin Manchester United a watan Janairu don samun inda zai ke buga wasa akai-akai ko Ingila ta gayyace shi gasar cin kofin duniya. Ana alakanta dan kwallon da Barcelona da kuma AC Milan. (Mirror)
Liverpool ta nuna sha'awar sayen dan wasan Leeds United, Raphinha a lokacin cinikin 'yan wasa in ji mai kula da harkokin wasanninsa, Deco. (Globo Esporte - in Portuguese)
Kocin Arsenal, Mikel Arteta yana da 'yan kwallon da ke son dauka nan gaba da suka hada da mai tsaron bayan Brighton, Tariq Lamptey da dan wasan Leicester City, James Justin da na Norwich City, Max Aarons. (Fichajes - in Spanish)
Fenerbahce na son sayen dan kwallon Tottenham, Ryan Sessegnon a watan Janairu. (Sun)
Tottenham tana cikin masu son zawarcin mai tsaron bayan Stoke City, Harry Souttar, wanda tuni Aston Villa ta dade tana bibiyar dan k