Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ballon d'Or: Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Robert Lewandowski na cikin ƴan wasa 30
Jorginho na Chelsea na cikin ƴan wasa 30 da ke takarar lashe kyautar Ballon d'Or ta bana, da suka ƙunshi ɗan wasan Paris St-Germain Lionel Messi da Robert Lewandowski na Bayern Munich.
Messi ne ya lashe kyautar a 2019 karo na shida.
A karon farko, ɗan wasan ya lashe wa ƙasarsa kofi inda ya taimaka wa Argentina lashe Copa America na 2021.
Ɗan wasan tsakiya na Italiya Jorginho ya taimakawa Chelsea lashe kofin zakarun Turai kafin ya lashe wa ƙasarsa kofin Turai na Euro 2020.
Ɗan wasan gaba na Poland, Robert Lewandowski, da ke taka leda a Bayern Munich ne ya lashe takalmin zinari a Turai a kakar 2020-21 a matsayin wanda ya fi cin ƙwallaye a raga, bayan ya zira 41 tare da taimaka wa Bayern Munich lashe Bundesliga.
Cristiano Ronaldo na Manchester United wanda ya lashe kyautar sau biyar, na cikin ƴan wasa 30 da aka zaɓa domin lashe kyautar ta Ballon d'Or ta bana.
Akwai kuma Luka Modric wanda ya ratso tsakanin Messi da Ronaldo ya lashe kyautar a baya.
Akwai ƴan wasa 14 na Premier League cikin ƴan wasa 30 da aka zaɓa da kuma ƴan wasan Italiya da suka lashe kofin Turai.
Akwai kuma ƴan wasan PSG; Neymar na Brazil da Mbappe na Faransa.
Mujallar Faransa ce ke bayar da kyautar Ballon d'Or duk shekara.
A 2020 ba a bayar da kyautar ba saboda annobar korona - karon farko tun 1956.
A ranar 29 ga watan Nuwamba ne za a sanar da wanda ya lashe kyautar a birnin Paris.
Ɗan wasan Ingila Jude Bellingham na Borussia Dortmund da Mason Greenwood na Manchester United da Bukayo Saka na Arsenal, na cikin ƴan wasa 10 da ke takarar lashe kyautar gwarzon matashin dan wasa na duniya ta Kopa Trophy, wadda ake ba i wa ƴan ƙasa da shekara 21.
Ana bai wa kuma masu tsaron raga Kyautar Yashin, kuma masu tsaron raga 4 ke takarar lashe kyautar daga gasar Premier League. Sun haɗa da golan Chelsea da Senegal, Edouard Mendy, da na Manchester City da Brazil, Ederson, da na Leicester City da na Denmark, Kasper Schmeichel, da kuma na Aston Villa da Argentina Emiliano Martinez.
Ƴan wasa 30 da ke takarar lashe Ballon d'Or
Cesar Azpilicueta (Chelsea, Spain)
Nicolo Barella (Inter Milan, Italiya)
Karim Benzema (Real Madrid, Faransa)
Leonardo Bonucci (Juventus, Italiya)
Kevin de Bruyne (Manchester City, Belgium)
Giorgio Chiellini (Juventus, Italiya)
Ruben Dias (Manchester City, Portugal)
Gianluigi Donnarumma (PSG, Italiya)
Bruno Fernandes (Manchester United, Portugal)
Phil Foden (Manchester City, Ingila)
Erling Braut Haaland (Borussia Dortmund, Norway)
Jorginho (Chelsea, Italiya)
Harry Kane (Tottenham, Ingila)
N'Golo Kante (Chelsea, Faransa)
Simon Kjaer (AC Milan, Denmark)
Robert Lewandowski (Bayern Munich, Poland)
Romelu Lukaku (Chelsea, Belgium)
Riyad Mahrez (Manchester City, Algeria)
Lautaro Martinez (Inter Milan, Argentina)
Kylian Mbappe (PSG, Faransa)
Lionel Messi (PSG, Argentina)
Luka Modric (Real Madrid, Croatia)
Gerard Moreno (Villarreal, Spain)
Mason Mount (Chelsea, Ingila)
Neymar (PSG, Brazil)
Pedri (Barcelona, Spain)
Cristiano Ronaldo (Manchester United, Portugal)
Mohamed Salah (Liverpool, Masar)
Raheem Sterling (Manchester City, Ingila)
Luis Suarez (Atletico Madrid, Uruguay)
Mene ne Ballon d'Or?
Mujallar Faransa ta fara bayar da kyautar Ballon d'Or tun 1956, inda take karrama gwarzon ɗan wasan duniya, kuma ɗan wasan Ingila Stanley Matthews ne na farko da ya lashe kyautar.
Da farko ƴan wasan Turai ake ba kyautar kafin 1995 da aka faɗaɗa ga dukkanin ƴan wasan da ke taka leda a ƙungiyoyin Turai. Daga 2007 gasar ta koma ta duniya.
Ƴan jaridar mujallar Faransa ne ke zaɓen ƴan wasa 30, inda kuma sauran ƴan jarida a faɗin duniya za su zaɓi wanda zai lashe kyautar. Ko wace ƙasa a duniya tana da wakili ɗaya.
Daga 2010 zuwa 2015 aka haɗe kyautar da ta Fifa, amma daga baya suka rabu, inda Fifa ta ƙaddamar da kyautarta mai suna The Best a 2016.