Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Farashin kayan abinci ya tashi a duniya
Shugaban daya daga cikin manyan kamfanonin samar da kayan abinci na duniya na Kraft Heinz, ya ce kamata ya yi mutane su saba da tsadar kayan masarufi.
Miguel Patricio, ya shaida wa BBC cewa matsin tallatin arziki da hahhawar farashin kayayyaki sakamakon annobar cutar korona na daga cikin dalilan da lamarin ya yi kamari.
Ya kara da cewa kamfaninsa ya fuskanci tashin farashin kayayyakin da yake amfani da su wajen sarrafa kayan abinci, don haka dole abokan hulda su ma su fuskanci karin farashi.
Miguel Patricio, ya ce kara farashin kayayyakin na da nasaba da karancin direbobin manyan motocin da ke dakon kaya a Birtaniya, da kuma yadda farashin kayayyaki ya ke a Amurka baya ga annobar korona da ta ta'azzara tsadar kayayyaki a duniya baki daya.
Amma ya ce fasahar zamani da sabon Irin da ake da su ka iya taimakawa manoma su ƙara samun amfanin gona mai kyau.
Hukumar da ke kula da farashin kayan abinci ta majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa farashin kayan abinci a duniya ya yi tashin gwauron zabin da ba a taba gani ba cikin shekara goma, yayin da bukatar abincin ta ƙaru sakamakon karuwar jama'a da ake fuskanta.