Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko akwai jam'iyyar da za ta iya ƙalubalantar APC da PDP a Najeriya?
Bayanai daga Najeriya na nuna cewa yanzu haka wasu fitattun yan siyasa a kasar na gangamin kafa wata kungiya mai nasaba da siyasa.
Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Hukumar Zabe wato Farfesa Attahiru Jega, da kuma masanin kimiyyar siyasa da tattalin arziki Farfesa Pat Utomi da dai sauran wasu sanannun fuskokin.
Bayanai sun nuna cewa za su yi gangamin kaddamar da babbar kungiyar masu kishin kasa a ranar 1 ga watan Oktoba, wanda zai yi dai-dai da ranar da Najeriya ke cika shekara 61 da samun 'yancin kai.
Ana hasashen kungiyar za ta kunshi kungiyoyin siyasa da na masu fafutuka da suka hada da Rescue Nigeria Project, da Nigeria Intervention Movement da sauran kungiyoyi ire-irensu.
Kamar yadda wasu jaridun kasar suka ruwaito akwai tsari a kasa da gungun 'yan siyasar ke yi na mayar da kungiyar zuwa jam'iyar siyasa, da za ta kalubalanci manyan jam'iyyun kasar kamar APC mai mulki, da kuma babbar jam'iyar adawa ta PDP.
A na rade radin jam'iyyar Peoples Redemption Party ko kuma PRP da Attahiru Jega ya fito, da African Democratic Congress da Chief Ralph Nwosu ke Shugabanta daga Kudanci, da ma jam'iyyar Labour Party duk sun daura aniyar hadewa wuri guda don fara sabuwar tafiyar.
Tuni masana harkokin siyasa a kasar suka fara dubba yadda lamarin zai kasance.
A cewar Malam Kabir Sufi, mai fashin baki kan lamurran siyasa a Najeriya ''gangamin kafa sabuwar jam'iyya da za ta ja da manyan jam'iyyun Najeriya abu ne da wasu da ba su gamsu da akidun PDP da APC ba, kuma su ke ganin akwai bukatar fito da wata jam'iya da za ta maye gurbinsu.''
Sai dai kuma masanin na ganin akwai jan aiki ga hadakar kafin a iya cewa za ta iya gwa-gwa-gwa da manyan jam'iyyun kasar.
Waɗanne ƙalubale jam'iyyar za ta fuskanta?
A cewarsa daya daga cikin manyan kalubalan da hadakar za ta fuskanta shi ne ''samun hadin kan jam'iyyun da dama ke da shugabanci, don wasunsu za su rika tunanin 'me ce ce makomarsu idan suka hade'? wanda hakan zai haifar da jan kafa kafin su gama aminta da tafiyar.''
Masanin ya buga misali da kafuwar jam'iyar APC mai mulki a lokacin da a ka yi fadi tashin kafuwarta wadda a karshe ta kawo karshen mulkin jam'iyar PDP mai mulki a lokacin.
Haka kuma ya ce akwai bukatar yin nazari don fito da hanyoyin tallata jam'iyyar ya zama cewa ta karbu ga jama'a, da kuma shirin tunkarar barazana daga manyan jam'iyyun.
"A baya jam'iyyar PDP ta yi barazanar cewa babu wata jam'iyya da za a kafa da za ta iya kwatar mulki daga hannunta musamman a matakin gwamnatin tarayya.
''To amma duk da wannan barazana hakan bai hana a ka kafa jam'iyar APC ba, kuma har ta kai ga kafa gwamnati," a cewar Malam Kabiru Sufi.
"Saboda haka a yanzu ma ba za a yanke kaunar wannan kungiya ta siyasa za ta iya kai wa jam'iyya, kuma har ta kai matsayin babbar jam'iyya da za ta yi hamayya da su wadannan jam'iyu guda biyu kamar yadda a ka gani a baya", a cewar sa.
Manyan jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya, APC da PDP sun daɗe suna jan zaren mulki tun bayan komawa tsarin demokuradiyya a kasar a shekarar 1999.
Sai dai a baya-bayan nan, jam'iyyun biyu duk sun fara fuskantar matsaloli na shugabanci da na ficewar wasu jiga-jigan jam'iyyoyin suna komawa ɗaya bangaren.
Wani lamari da ake ta ce-ce-ku-ce a kai a kasar shi ne na rade-radin cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kuma jigo a jam'iyyar PDP zai koma jam'iyyar APC mai mulki, kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa sai dai babu tabbas kan wannan batu.
Haka kuma jigon jam'iyyar PDP kuma babban mai sukar gwamnatin APC, Femi Fani-Kayode ya sauya sheka kwanan nan zuwa jam'iyyar mai mulki- lamarin da ya bai wa ƴan Najeriya da dama mamaki.
Kafin nan, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya koma jam'iyyar APC daga ta PDP wadda ya yi nasarar hawa mulki da tutarta - a wani salo da ba a saba gani ba kuma, mataimakinsa Mahdi Ali Gusau na nan a jam'iyyar PDP, wato dai bai sauya sheka ba shi.
A nata bangaren a jam'iyyar APC, an samu rarrabuwar kai kan kwamitin riƙo wanda gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ke jagoranta.
Matsaloli ire-iren haka na ci gaba da kunno kai a jam'iyyun biyu, a lokaci guda kuma ƴan Najeriya da dama na ganin cewa a yanzu babu wani bambanci tsakanin manyan jam'iyyun biyu gnain cewa mafi yawansu yanzu a bangare ɗaya su ke.
Gabanin zaɓen 2023, kafuwar wata jam'iyya a Najeriya na iya bai wa ƴan ƙasar da ke cewa sun dawo daga rakiyar jami'yyun APC da PDP wani zaɓin yadda za su bayyana ra'ayinsu na zama cikakkun ƴan kasa ta hanyar yin zaɓe.