Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Najeriya na caccakar Femi Fani-Kayode kan komawa APC
Mamaki ya cika 'yan Najeriya da yawa bayan samun labarin sauya sheƙar da Femi Fani-Kayode ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki.
Mutumin da 'yan kasar ke yi wa kallon wanda ya fi kowa adawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC mai mulki a kasar a yanzu ya koma inuwa guda da abokin gabarsa.
Kalaman Femi wanda ake taƙaita sunansa da FFK, a baya sun rika faranta wa masu adawa da APC tare da muzanta wa gwamnati mai mulki da muƙarrabanta.
Wannan shi ne babban labarin da ya mamaye fuskar jaridun Najeriya a ranar Juma'a, yayin da da yawan 'yan kasar a kafafen sada zumunta su ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu.
Wani abu da ya fi bai wa 'yan kasar mamaki ya sa suke caccakar FFK shi ne cewar dalilinsa na komawa APC si ne don "Buhari ya sauya," a hirarsa da gidan talabijin na Channels a nara Alhamis, wato yana nufin ba Buharin da ya riƙa suka ba ne a baya.
Daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta, wani matashi da ake kira Mr Right@OtunMuri cewa ya yi:
"Zan so in ji dalilan FKK na koma wa APC. Watakila akwai dalilan da ba mu sani ba. Watakila hauhawar kaya ta ragu zuwa kashi 1 cikin 100 ne, kuma an fara shawo kan matsalar rashin aikin yi, ba mamaki dala ta dawo naira 100.
"Watakila miƙa kan da 'yan Boko Haram suke yi da kawo karshen 'yan bindigar daji ne ya sanya shi komawa! Ina so in ji yadda zai rera wannan waƙar.
Mayor of Jos @JonnieIledun kuma dauko wata maganar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi, inda yake cewa "FFK yarona ne. Ku ba shi abinci ya ci, zai ci sannan kuma ya yi muku waƙa."
Sai ya ƙara da cewa ya nuna cewa tabbas akwai yunwa a Najeriya, amma mene ne ya faru da jam'iyyar PDP?
Ya sanya wani tsohon sakon da FKK ya wallafa a shafinsa na Twitter a 2018:
"Mutumin da kuke gani a yau Jibril ne daga Sudan ba Buhari ba, Buhari ya mutu kuma bai dawo daga Landan ba, jikinsa ne kawai. Sun ciro ruhin Jibril ne suka sanya a gangar jikin Buhari.
"Wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare a wajen shaidanu, an sarayar da rayukan mutane da yawa."
Wani matashi mai suna @Real_Suleman ya sanya tsohon bayanin da FFK ya yi a 2019, lokacin da ya musanta labarin da aka rika yaɗawa cewa ya koma jam'iyyar APC.
A jikin saƙon FKK ya ce "Maganar da ake yada wa cewa na koma APC ba gaskiya ba ce, cin zarafi ne a wurina. Wadanda suke yaɗa wannan labarin ƙaryar sai su binne kansu a ƙasa don kunya.
"Da waɗannan abubuwan da muke gani na gwammace na mutu da na koma APC me kamar wani kwale-kwale da ke cike da beraye masu cututtuka."
Dawowa daga rakiyar 'yan siyasa?
Da yawan 'yan Najeriya na sharhi ne kan salon 'yan siyasar kasar. DUk da dai a kan ce siyasa ba da gaba ba, amma suna ganin a yani irin na FKK akwai daure kai da al'ajabi.
Masu sharhi da dama ma cewa suke yi sun dawo daga rakiyar 'yan siyasa da "rikita-rikitarsu".
Muhsin Ibrahim wani dan Najeriya kuma malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus ya ce wallafa a shafinsa na Facebooj cewa:
"Femi Fani-Kayode ya koma APC? Bbau wani abin mamaki a nan, Ganin yadda abubuwa ke wakana a Najeriya a yau, ina shakkar idan har akwai wani abin da zai sake kada ni.
Dukkanmu mun damu ne a kan abu daya: ta yaya za mu gyara miyarmu. Duk wani abu bayan haka, ko da batun gyran kasar ne a misali, to bayan wannan zai biyo ko ma mara amfani ake ganinsa.
APC da FFK burinsu daya ne, kuma shi ne ci gaba da durkusar da kasar nan. Don haka, sun cimma yarjejeniya. Mafi yawanmu da muke sukar (APC & FFK) watalika muma ba za mu iya watsi da irin wannan damar ba in an ba mu. Wasu da yawa sun yi hakan a baya."
Shi ma Idiris Hamza Yana, malami a Jam'iar Kafin-Hausa a jihar Jigawa, kuma mai kartun digiri na uku a wata jami'a a Birtaniya ya wallafa a Facebook cewa:
"Ban yi mamaki ko jin takaicin komawar FFK zuwa jam'iyyar APC ba. A takaice ma, farin ciki na ji da hakan.
"Ga alama APC na neman wawan jam'iyya ne mai baki da zai dinga yi mata aikin caccakar manyan 'yan siyasar yankin kudu maso yamma.
"Shekarar 2023 za ta yi armashi."
In kaga kare na shinshina takalmi..............
Cikin 'yan Najeriya da ke bibiyar siyasar sau da kafa, komawar FFK APC bai zo muku da mamaki ba, saboda wasu alamomi da suka riƙa gani.
Tun daga watan Agustan da ya gabata, ake ta ganin yadda FFK yake tashi fadin bibiyar mambobin jam'iyyar APC daga masu mukamansu har wadanda ba su rike da komai.
Ga jerin sakonnin da yake wallafawa na nuna goyon baya ga wannan gwamnatin a yaƙin da take yi da 'yan tada kayar baya da masu satar mutane da 'yan bindiga.
A ranar 16 ga watan Agusta, FFK ya wallafa cewa ya kai wa dan uwansa Sanata Ahmad Sani Yarima kuma tsohon gwamnan Zamfara ziyara gida inda zuka tattauna kan batutuwan da za su ciyar da Najeriya gaba.
Sai a ranar 19 ga watan Agustan inda ya wallafa wasu hotuna na daurin auren dan gidan shugaban Najeriya Yusuf Muhammadu Buhari da aka yi a Kano.
Ya ce sun tafi Kano daurin aure tare da 'yan uwa da abokan arziki kamar Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara da Gwamna Babagana Umar Zulum na Borno da Sanata Sani Ahmed Yarima da Sanata Ali Ndume da Ambasada Bashir Yuguda da Minista Isa Pantami da Mallam Nuhu Ribadu da dai sauransu.
FFK ya sanya hotuna da bidiyon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle a shafukansa masu yawa, a wasu wuraren suna cin abinci tare a wasu kuma ya kai masa ziyara Gusau babban birnin Jihar ta Zamfara, wanda wadannan duka abubuwa ne da ba kasafai ake gani ba a wurinsa.
Ya ziyarci Jihar Filato domin tattaunawa da gwamnan jihar Simon Lalong, bayan samun rikicin da aka yi tsakanin mabiya addinin Muslunci da na Kirista.
Ya ce maƙasudin ziyarar shi ne jajanta wa da kuma addu'ar neman zaman lafiya mai dorewa a jihar, wadda ake fama da dokar kulle a cikinta saboda rikicin.
Abin bai tsaya iya nan ba, ya ci gaba da yabon wannan gwamnatin a fakaice, inda a wasu jerin sakonninsa da yake yi akai-akai a Twitter yake yabon sojojin Najeriya kan yakin da suke yi da kuma nasarar da ake ikirarin suna samu a Jihar Zamfara.
"Ku ci gaba da kutsawa yara, ku yake su da duka karfin da kuke da shi, muna gode muku saboda kwarin gwiwarku da kuma sadaukarwarku. Dukkan yabo ya tabbata da Allah."
Kwatsam sai a ranar Alhamis abin da ake jira ya faru ya faru, labarin komaway FFK APC, hotunansa suka baza ko ina a fadin ciki da wajen Najeriya.
Jaridun ƙasar da dama sun rika yin babban labarinsu da cewa " wanda ya fi sukar jam'iyyar APC mai mulki ya koma cikinta".
Wasu kalaman Femi Fani-Kayode na baya
Wannan daya ne daga cikin kalaman FFK wadanda suka fi shahara kuma suka kara bunkasa lokacin da ake yi masa cin fuska bayan komawarsa jam'iyyar APC.
"Maganar da ake yada wa cewa na koma APC ba gaskiya ba ce, cin zarafi ne a wuri na.
"Wadanda suke yaɗa wannan labarin ƙaryar sai su binne kansu a ƙasa don kunya. Da waɗannan abubuwan da muke gani na gwammace na mutu da na koma APC me kamar wani kwale-kwale da ke cike da beraye masu cutuka," in ji FFK.
Wasu da yawa na cewa tuni Femi ya goge wannan sako daga cikin jerin sakunansa da ya taba wallafawa.
Wannan sakon na daga cikin wadanda suka janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya a 2018, lokacin da shugaba Buhari ya tafi Landan domin a duba lafiyarsa.
Femi ya rubuta cewa "Mutumin da kuke gani a yau Jibril ne daga Sudan ba Buhari ba, Buhari ya mutu kuma bai dawo ba daga Landan, Jikinsa ne kawai. Sun ciro ruhin Jibril ne suka sanya a gangar jikin Buhari. Wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare a wajen shaidanu, an sarayar da rayukan mutane da yawa."
Sharhi daga Buhari Muhammad Fagge
Mafi yawan abubuwan da Femi Fani-Kayode ya rika yin tsokaci a kansu musamman na harkokin tsaro babu abin da ya sauya a cikinsu sai dai ta'azzara da suka yi, idan aka kwatanta da yadda al'amura suke a 2015 zuwa 2019 lokacin da aka ƙara zaban wannan gwamnati mai ci ta Najeriya.
Tambayar da take zuwa cikin zukatan mutanen kasar a mafi yawan lokuta tun bayan samun labarain komawar FFK APC ita ce, shin al'amura ne suka sauya yadda yake fatan gani ko kuma me?
An samu sauƙin rayuwa ne sama da a baya ko kuma adadin marasa ayyukanyi ya ragu a Najeriya? Shin akwai wani gagarumin abu da wannan gwamnati ta yi da ya janyo hankalin FFK ya koma jam'iyyar?
Wadannan dai suke tambayoyin da har yanzu babu wanda yake da amsarsu.
Ko da yake a irin wannan yanayin siyasar da ake yi a Najeriya ta neman abin sa wa a baka, ba ta aƙida ba, za a iya zawarcin FFK zuwa APC, ko kuma shi a raɗin kansa ya ji cewa gwara ya koma domin bayar da gudunmawarsa ta ciyar da Najeriya gaba, Tunda a yanzu ya ce "Buhari ya sauya".