Mutum 300 sun hallaka a girgizar ƙasa a Haiti

Girgizar ta lalata gidaje da dama

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Girgizar ta lalata gidaje da dama
An wallafa

Girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske ta afkawa ƙasar Haiti da ke yankin Caribbean, inda ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 300.

Girgizar kasa mai karfin maki 7.2 ta faru ne a yammacin kasar da safiyar Asabar, inda ta ruguje tare da lalata gine-gine da suka hada da majami'u da otal-otal.

Firayim Ministan kasar ya ce akwai "barna mai yawa" a wasu yankuna, kuma ya ayyana dokar ta baci na tsawon wata guda.

Haiti na ci gaba da farfadowa daga mummunar girgizar kasa ta shekarar 2010.

Girgizar kasar ta ranar Asabar ta fi tasiri ne a wani wuri mai nisan kilomita 12 da garin Saint-Louis du Sud, in ji hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka

An ji girgizar ƙasa a babban birnin Port-au-Prince mai yawan jama'a, mai nisan kilomita 125 da kuma kasashe makwabta.

Christella Saint Hilaire, wacce ke zaune kusa da wurin da abin ya faru, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "Gidaje da yawa sun lalace, mutane sun mutu wasu kuma suna asibiti."

Firayim Minista Ariel Henry ya ce ya haɗa wata tawaga don yin aiki kan samar da agaji.

Naomi Verneus, 'yar shekara 34, na zaune ne Port-au-Prince babban birnin kasar, ta kuma shaida wa kamfanin dillacin labarai na AP cewa girgizar kasa ta farkar da ita kuma gadonta ya rika girgiza.

"Na farka kuma ba ni da lokacin da zan sanya takalmina. Mun tsira a girgizar ƙasa ta 2010 kuma abin da zan iya yi shi ne gudu.

''Daga baya na tuna yara na biyu da mahaifiyata suna ciki. Maƙwabcina ya shiga ya ce su fito. Mun gudu a kan titi. "inji ta.

Girgizar ƙasar da ta faru a Haiti a 2010 ta kashe mutum sama da 200,000 tare da haddasa ɓarna mai yawa ga kayayyakin more rayuwa da tattalin arziki.

Girgizar ƙasar ta ranar Asabar na zuwa ne yayin da Haiti ke fama da rikicin siyasa, bayan kisan shugabanta a watan da ya gabata.