Coronavirus: Yadda za ku yi rijistar karɓar riga-kafin cutar korona a Najeriya

An wallafa

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani tsari don bijiro da aikin allurar riga-kafin korona rukuni-rukuni da nufin tabbatar da adalci wajen rabonta a ƙasar.

Shirin mai taken TEACH, hukumar bunƙasa lafiya a matakin farko da haɗin gwiwar ma'aikatar lafiya ne suka ɓullo da shi.

Dr Abdullahi Bulama Garba daraktan tsare-tsare, bincike da tattara alkaluma a hukumar, ya shaida wa BBC cewa Najeriya ta fitar da tsarin ne don yi wa al'ummarta allurar daki-daki, ko da yake ya ce jami'an lafiya ne a kan gaba-gaba.

Rukuni na biyu bayan ma'aikatan lafiya, a cewar Dakta Garba shi ne manyan ƙasa - yi musu zai sa mutane su ƙara yadda da rigakafin. "Za a haɗa su da mutanen da suka wuce shekara 50 saboda yawancin korona da take kisa su ne waɗan nan da suka wuce shekara 50".

"A yanzu, ba ma sa mata masu ciki ko yara ƙasa da shekara 18 ba don wani abu ba saboda kowa ya san cutar nan sabuwa ce, kuma bincike ake ta yi kuma kowa ƙoƙari yake ya fahimce ta," in ji Dakta Garba.

Jami'in ya bayyana cewa rukunin ƙarshe zai kasance sauran jama'ar gari daga shekara 18 zuwa sama.

Tsarin karɓar allurar riga-kafin

Daraktan tsare-tsare, bincike da tattara alkaluma a hukumar bunƙasa lafiya a matakin farko ya ce "a cikin shirye-shiryen da muke yi yanzu haka, mun riga mun yi bita, mun tura mutane, daga Abuja da waɗanda suke taimakawa muke aikin nan tare, za a je matakin TEACH, muna son mu samu alƙaluman mutanen da ya kamata a yi wa".

Ya ce a yanzu haka, an buɗe dama domin yin rajistar karɓar rigakafin cikin sauƙi ta wannan shafin - "za ka sa suna da lamba da ranar da mutum yake so a yi masa allurar".

Ga waɗanda ba su da wayar hannu da za su iya rijistar, jami'in ya ce an yi tanadin jami'an da za su riƙa bi gida-gida domin yi wa jama'a allurar.

A cewarsa, za a fara aikin yin allurar riga-kafin ta cutar korona daga ranar 12 ga watan Maris.