Ethiopia: Yadda Habasha ta ɗaure ƙananan yara a gidan yari

An wallafa

Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Habasha (EHRC) ta ce ta gano kananan yara a tsare a wasu gidajen yarin ƙasar da aka tsare duk da ƙarancin shekaru, saboda zargin 'yan kungiyar tayar da kayar baya ne.

A wata sanarwa a ranar Litinin EHRC ta ce ta gano yaran ne a jihar Gambella da ke kudu maso yammacin kasar yayin ziyarar gani da ido da suka kai a watan da ya gabata.

Yaran masu shekaru tsakanin 11 zuwa 14 'yan kungiyar Oromo Liberation Army (OLA) ne a cewar ƙungiyar.

A shekarun baya bayan nan dai ayyukan ƙungiyar sun nuna yadda take al'amuran ta bisa cin gashin kai ba tare da wani shshigi ba, duk da alaƙar da ke akwai tsakaninta da bangaren gwamnati.

Hukumar ta ce an rika jibgar wasu yara maza biyu masu shekaru 11 da 12 da wata yarinya 'yar shekaru 14, bayan shafe kusan wata guda a kulle.

Ita dai kungiyar OLA wacce hukumomi ke yawan kiranta da OLF Shane kungiya ce da ta balle daga kungiyar neman yanci ta Oromo Liberation Front (OLF) kuma ana ganin tana aiki a yammacin Habasha.

Hukumar ta kuma ce an daure mutane 90 yan Tigray a jihar tun farkon watan Nuwamba.

An zarge su da tallafawa kungiyar Tigrayan People's Liberation Front (TPLF) wacce ta yi yaƙi da sojojin tarayya a arewacin Habasha.

Sun kasance a hannun 'yan sanda kuma babu wani bincike da aka gudanar, in ji EHRC.

Daniel Bekele, wani jami'i daga hukumar, ya kara da cewa "batun tsare yara, da kuma tabbatar da belin wadanda ake tsare da su na bukatar kulawa ta gaggawa."

A baya bayan nan ne aka samu rahoton zarge-zarge masu karfi na cin zarafin mata a yankin Tigray na arewacin Habasha, ciki har da laifin fyade a garin Mekelle, in ji wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafi yayin yaki.

Sojojin gwamnati sun kwace iko da Mekelle, babban birnin yankin, a ranar 28 ga Nuwamba bayan an kwashe makonni ana fada.

Misis Patten ta ce: "Akwai kuma rahotanni masu tayar da hankali na mutanen da ake zargin an tilasta musu yi wa danginsu fyade, bayan an musu barazana.

"Wasu rahotanni sun ce wasu sojoji ma sun tilasta wa mata yin lalata da su kafin ba su abinci.